An tashi baktatan a makaranta bisa tsoron harin 'yan bindiga a jihar Imo
- Tsoron harin yan bindiga ya tursasa makarantu sallamar dalibai a garin Owerri, babbar birnin jihar Imo
- An tattaro cewa an rufe makarantun ne sakamakon wata wasika da ke ta yawo a shafukan sadarwa inda aka yi gargadin cewa za a farmaki duk makarantar da ta bude a ranar Litinin
- Hakazalika hare-haren da yan bindiga suka kai ofishoshin yan sanda a makon da ya gabata ya kara rura wutan tsoro a zukatan mazauna jihar
Imo - Wasu makarantu a birnin Owerri sun tsayar da harkoki cak a ranar Litinin, 21 ga watan Maris, sannan suka tursasa dalibai komawa gidajensu kan zargin cewa wasu yan bindiga da ba a san ko su waye ba za su kai masu hari.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa iyaye sun cika da zullumi yayin da suke kwasan yaransu zuwa gida.
Wasu daga cikin shugabannin da ba a bayyana sunayensu ba saboda dalilai na tsaro, sun bayyana cewa dole suka rufe makarantunsu saboda wata wasika da ta yi fice a shafukan soshiyal midiya wacca aka alakanta da yan bindigar da ba a sani ba.
Wasikar ta yi gargadin cewa ba za a kuma yin zirga-zirga ba, sannan za a dunga rufe makarantu a duk ranar Litinin a kasar Inyamurai.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewarsu:
“Za a kai farmaki ga duk makarantar da ta ki bin umurnin.”
Rahoton ya kuma nuna cewa tuni wasu makarantu a hanyar Egbu, Akwakuma, Amakohia, hanyar Owerri-Aba, hanyar Akwakuma, Amakohia, Owerri-Aba suka rufe makarantunsu saboda tsoro.
Lamarin ya kuma shafi wasu makarantu a hanyar MCC/Uratta, hanyar Okigwe zuwa yankin Orji da kuma yankunan bankin duniya.
Hakazalika, a safiyar yau Litinin, akwai karancin mutane da ababen hawa da ke zirga-zirga a cikin birnin na Owerri.
Wasu daga cikin mazauna birnin da suka yi magana, sun ce hare-haren da aka kai kan ofishoshin yan sanda da gine-ginen mutane ya haifar da tsoro wanda shine ya sa mutane suka yanke shawarar zama a gida.
A cewar wata Tobe Ugwuegbu, mazauniyar Wethedral:
“Hare-hare da suka kai ofishoshin yan sanda daba-daban ciki harda kisan jami’an yan sanda ya dasa tsoro a zukatan mutane inda suke ganin zaman gida na ranar Litinin zai zama mai hatsari.
“Wannan ne dalilin da yasa kuke ganin unguwanni sun zama kamar kufai kowa na zaune a cikin gidajensu. Babu wanda ke so a kashe shi.”
Yan sanda sun kashe yan bindiga 4, sun gano bama-bamai 5 da ba a tayar ba
A wani labarin, mun ji a baya cewa rundunar yan sandan jihar Imo ta kashe yan bindiga biyar da ake zaton yan kungiyar awaren IPOB ne a wani musayar wuta da suka yi a safiyar Lahadi, 20 ga watan Maris.
Lamarin ya faru ne lokacin da yan bindigar suka je kai farmaki ofishin yan sanda da ke karamar hukumar Oru East a jihar Imo.
Kakakin yan sandan jihar, Micheal Abattam, ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Owerri, babbar birnin jihar, jaridar Vanguard ta rahoto.
Asali: Legit.ng