Wani Da Ke Sallah a Masallacin Da Na Ke Limanci Ya Ɗirka Wa Matata Ciki, Liman Ya Faɗa Wa Kotu
- Wani limamin masallaci a garin Oyo jihar Ibadan ya yi zargin wani daga cikin mamunsa ya ɗirka wa matarsa ciki
- Limamin ya ce tunda matarsa ta tambaye shi kudi domin ta bude shago ya nuna ba shi da shi sai ta fara fanɗare masa daga baya ta bar gidansa
- A bangarenta, matar ta ce limanin ba shi da halaye masu kyau kuma yana kawo mata gida, ta bar gidansa don tsira da ranta
Oyo - Alhaji Lukman Shittu, wani malamin addinin musulunci a Oyo ya yi zargin cewa wani daga cikin wadanda suke sallah a masallacinsa ya ɗirka wa matarsa ciki, Daily Trust ta ruwaito.
Ya yi wannan zargin ne yayin da ya ke bayani ga kotun kwastamare Grade A da ke zamanta a Mapo, Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
Shittu, wanda matarsa ta yi kararsa na neman saki, ya shaida wa kotun cewa matarsa tana bin mazaje kuma ta haifi ƴaƴa uku da bai da tabbas nasa ne, rahoton Daily Trust.
Nan take bayan sauraron wannan ikirarin, alkalin kotun S.M. Akintayo ya bada umurnin su tafi asibiti su yi gwajin ƙwayar hallita ta DNA don sanin idan Shittu ne mahaifin ya'yan ko ba shi bane.
Alkali ya ce matar da mijin su hada kudi su biya gwajin DNA
Akintayo ya ce:
"Shittu da Fisayo za su hada kuɗi su biya gwajin DNA ɗin kuma za a tura wa kotu sakamakon gwajin kai tsaye".
Ta dage cigaba da shari'ar zuwa ranar 2 ga watan Mayu domin gabatar da sakamakon DNA.
Tunda farko, Shittu ya shaida wa kotu cewa matarsa ta fara tuƙa zuƙeƙiyar mota jim kaɗan bayan ta bar gidansa a 2021.
Ya ce:
"Duk da cewa Fisayo tana alfahari cewa ɗan uwanta ne ya bata kyautan motar. Binciken da na yi ya nuna min cewa, mutumin da suka dade suna baɗala tare ne ya siya mata motar.
"Fisayo ta fara rashin ji ne bayan na gaza bata kuɗi to karbi hayan shago. Daga nan, ta fara dawowa gida latti kuma na faɗa mata zan rufe ta a gida idan ta sake yin hakan."
Amma, sai Fisayo ta kwashe kayanta daga gida na tare da yaran uku.
"Ta canja wa na karshen makaranta ba tare da sani na ba, sauran biyun kuma sun ce daga yanzu sun dena ɗauka na a matsayin mahaifinsu.
"A watan Ramadan da ta gabata, na gayyaci ɗan mu na biyu ya zo wuri na amma ya ƙi. Shima na farkon ya ƙi zuwa gida na a lokacin da suka samu hutun makaranta. Ko ka san cewa dadiron na Fisayo a masallacin da na ke limanci ya ke sallah?"
Fisayo ta yi zargi cewa Shittu yana neman mata kuma ya yi barazanar halaka ta
Da farko, Fisayo wacce ta shigar da karar, mai zaune a Odo Ona Elewe a Ibadan, ta ce mijinta ba shi da halaye masu kyau kuma barazana ne a gare ta.
Ta ce:
"Shittu ya ruɗe ni na karɓo bashi daga banki da sunan zan bude shago ba tare da na biya ba. Domin ya samu kawo mata gidansa, Shittu ya yi barazanar zai daɓa min wuka idan ban bar gidansa ba.
"Bayan haka, ya kan kowa mata daban-daban gidan mu na aure.
"Bugu da ƙari, Shittu ya rushe shagon da na gyara da kuɗi na don kawai kada in yi kasuwanci.
"Yana zagi na da sunaye daban-daban kuma ya taba cewa ƴaƴan mu ba nasa bane.
"Duk da cewa yan uwan mu sun shiga tsakani, amma na bar gidansa domin in tsira."
Magidanci Ya Lakaɗa Wa Likitan Fata Mugun Duka Saboda Yaba Kyawun Fatar Matarsa
A wani labarin daban, 'yan sanda sun kama wani mutum bayan ya lakada wa likita dukan tsiya inda ya bar shi a mawuyacin hali bayan yabon kyawun fatar matar sa.
Matar wacce musulma ce mai sanye da hijabi ta sanar da mijinta, Bakhriddin Azimov cewa likitan fatar dan asalin kasar Rasha, Vladimir Zhirnokleev ya yaba kyawun fatarta.
Daga nan ne mutumin ya kai wa likitan farmaki, yanzu haka yana fuskantar hukunci akan cin zarafi kamar yadda LIB ta ruwaito.
Asali: Legit.ng