Da dumi-dumi: Yan sanda sun kashe yan bindiga 4, sun gano bama-bamai 5 da ba a tayar ba

Da dumi-dumi: Yan sanda sun kashe yan bindiga 4, sun gano bama-bamai 5 da ba a tayar ba

  • Jami'an yan sanda sun yi gagarumin nasara a kan yan bindiga a jihar Imo
  • Sun yi musayar wuta da maharan a safiyar Lahadi, 20 ga watan Maris, inda suka kashe yan bindiga hudu
  • Jami'an tsaron sun kuma kwato bama-bamai da ba a riga an tayar ba har guda biyar daga yan ta'addan

Imo - Rundunar yan sandan jihar Imo ta kashe yan bindiga biyar da ake zaton yan kungiyar awaren IPOB ne a wani musayar wuta da suka yi a safiyar Lahadi, 20 ga watan Maris.

Lamarin ya faru ne lokacin da yan bindigar suka je kai farmaki ofishin yan sanda da ke karamar hukumar Oru East a jihar Imo.

Kakakin yan sandan jihar, Micheal Abattam, ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Owerri, babbar birnin jihar, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Sojoji sun ragargaji mafakar 'yan Boko Haram da ISWAP, sun ceto mutane 30

Da dumi-dumi: Yan sanda sun kashe yan bindiga 4, sun gano bama-bamai 5 da ba a tayar ba a Imo
Yan sanda sun kashe yan bindiga 4, sun gano bama-bamai 5 da ba a tayar ba a Imo Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Ya kuma bayyana cewa an gano wasu bama-bamai biyar da ba a tayar ba daga hannun yan bindigar wanda ya ce yana a hannun sashin bama-bamai na yan sanda, Channels TV ta rahoto.

Rundunar yan sandan ta ci gaba da cewa jami’anta na aikin kakkabe dazuzzuka domin gano sauran yan bindigar da suka tsere da munanan raunuka da suka ji a yayin musayar wuta.

Yadda lamarin ya afku

Da take bayanin musayar wutan da suka yi da yan ta’addan, rundunar yan sandar ta ce:

“Sakamakon gyara da kuma karfafa dabarun da rundunar ke yi a karkashin kulawar kwamishinan ‘yan sanda na jihar Imo, CP Rabiu Hussaini psc, don dakile duk wasu ayyukan ta’addanci a cikin jihar musamman hare-hare kan ofishin ‘yan sanda.

Kara karanta wannan

Yan sanda da Sojoji sun yi wa yan bindiga rubdugu a Abuja, sun ceto mutum ɗaya

“A ranar 20 ga Maris, 2022 da misalin karfe 0300, ‘yan bindigar da ake zaton ‘yan kungiyar awaren IPOB ne sun zo ofishin ‘yan sanda na Omuma su da yawa dauke da bama-bamai, suna ta harbi kan mai uwa da wabi, amma tawagar yan sanda da na DSS sun gaggauta dakile cikin kwarewa da dabara.
“Jami’an yan sandan sun yi musayar wuta da yan bindigar kuma a cikin haka ne suka kashe mutum hudu daga cikinsu a nan take yayin da sauran suka gudu jeji bayan sun sha kaye, da damansu sun ji rauni sakamakon harbin bindiga. Yayin da a bangaren jami’an tsaro na hadin gwiwar ba a rasa kowa ba.
“A nan wajen, an kwato bama-bamai iri-iri daga wajen yan bindigar da aka kashe da kuma layuka. An mika bama-baman ga sashin yan sanda da ke kula da bama-bamai."

Da Duminsa: Ƴan Bindiga Sun Jefa 'Bam' Cikin Ofishin Ƴan Sanda, Sun Kashe Jami'ai 2, Sun Ƙona Motocci

Kara karanta wannan

Neja: Ƴan Bindiga Sun Ji Ba Daɗi A Hannun Jami'an Tsaro, Fiye Da 100 Sun Baƙunci Lahira

A wani labarin, mun ji cewa Yan sanda biyu sun mutu yayin da yan bindiga suka kona caji ofis a Umuguma a karamar hukumar Owerri West ta Jihar Imo, Rahoton Daily Trust.

Harin na zuwa ne awanni bayan mataimakin sufeta janar na yan sanda mai kula da zone 9, a Umuahia, Isaac Akinmoyede, ya bar jihar bayan ziyarar aiki na kwana daya.

An rahoto cewa a lokacin da maharan suka iso sun toshe hanyoyin shiga da fita ofishin yan sandan, har da wanda ke kusa da hedkatar karamar hukuma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng