Abin da Matar Gwamna mai barin-gado ta fada, har Bianca Ojukwu ta mare ta a taro

Abin da Matar Gwamna mai barin-gado ta fada, har Bianca Ojukwu ta mare ta a taro

  • Sabanin da aka samu tsakanin Madam Ebelechukwu Obiano da Bianca Ojukwu ya jawo surutai
  • Ana tunanin kalaman Ebelechukwu Obiano ne suka jawo Miss Ojukwu ta sharara mata mari a fuska
  • Da alama Kalaman tsohuwar uwar gidar gwamnan na Anambra ne suka fusata bazawarar Ojukwu

Anambra - Legit.ng ta samu karin bayani a game da abin da ya jawo rikici ya barke tsakanin Ebelechukwu Obiano da Bianca Ojukwu a ranar Alhamis.

Wadannan manyan mata biyu sun kicime da fada yayin da abin ya kai ga mari a lokacin da ake rantsar da Farfesa Charles Soludo a matsayin sabon gwamna.

Ana zargin Madam Ebelechukwu Obiano ce ta tsokano Miss Bianca Ojukwu a wajen taron bayan ta fada mata wasu kalamai da sam ba su yi mata dadin ji ba.

Kara karanta wannan

'Karin Bayan: Soludo Ya Yi Magana Kan Marin Da Matar Obiano Ta Yi Wa Bianca Ojukwu a Wurin Taron Rantsar Da Shi

Idan wannan labari ya tabbata, da uwargidar tsohon gwamna Willie Obiano ta karaso inda Ojukwu ta ke zaune ne, sai ta tambaye ta abin da ya kawo ta.

Abin bai tsaya nan ba, sai aka ce Ebelechukwu Obiano ta fadawa Bianca Ojukwu cewa tun farko ba ta so mai gidanta ya zama gwamnan jihar Anambra ba.

A jiyan ne wa’adin Willie Obiano ya cika bayan ya shafe shekaru takwas yana mulki a Anambra. Obiano ya yi mulki ne tun 2014 a karkashin jam’iyyar APGA.

Bianca Ojukwu
Bianca Ojukwu ta mari Ebelechukwu Obiano Hoto: legit.ng
Asali: UGC

Bakar magana ta jawo mari

A karshe sai aka ce Ebelechukwu Obiano ta kira Miss Ojukwu da kalmar mutumiyar banza.

Wannan magana da tsohuwar uwargidar jihar Anambra ta fada ne ya kara fusata Ojukwu, nan ta ke ta kai wa maidakin Obiano mari ana cikin tsakiyar taro.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Matar tsohon gwamna Obiano ta shararawa Bianca Ojukwu mari a wajen rantsar da Soludo

Amma an ce matar Marigayi Chukwuemeka Odumegwu-Ojukwu ta maidawa Obiano martani da bakaken kalamai, kafin ta sharara mata mari a gaban jama'a.

“Me ki ke yi a nan?
“Na dauka kin ce babu abin da zai kara hada ki da jam'iyyar APGA?
“Ki bar nan wurin, mutumiyar banza.”
“Ke mutumiyar banza ce.”

Mutum 50 aka gayyata

Ku na da labari cewa mutane 50 kadai Farfesa Charles Chukwuma Soludo ya gayyata su halarci bikin rantsuwarsa a Awka, inda ya gaji Gwamna Willie Obiano.

Watakila sabon gwamnan ya yi hakan ne domin gudun gwamnati ta kashe kudi masu yawa a wajen biki. A karshe dai da abin kunya aka tashi wannan taron.

Asali: Legit.ng

Online view pixel