Yanzu-Yanzu: Sojojin Rasha sun kashe wani fitaccen dan jaridar Amurka a Ukraine

Yanzu-Yanzu: Sojojin Rasha sun kashe wani fitaccen dan jaridar Amurka a Ukraine

  • A karon farko tun fara yakin Rasha da Ukraine an hallaka wani dan jaridar kasar Amurka a cikin Ukraine
  • Rahotanni sun bayyana cewa, sojojin Rasha ne suka hallaka dan jaridar a yau Lahadi 13 ga watan Maris
  • Brent Renaud, dan jarida ne da ya yi a jaridar New York Times, kana kwararren mai shirya fina-finai

Ukraine - 'Yan sanda sun ce an harbe wani fitaccen dan jaridar kasar Amurka da ke aiki a Ukraine a garin Irpin da ke wajen Kyiv, rahoton BBC.

Brent Renaud, mai shekaru 50, dan jarida ne kuma mai shirya fina-finai wanda a baya ya yi aiki da jaridar New York Times.

Shugaban 'yan sandan Kyiv Andriy Nebytov ya ce sojojin Rasha ne suka kai masa hari, kana wasu ‘yan jarida biyu sun jikkata kuma an kai su asibiti a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Gano Ƙananan Yara Ƴan Shekaru 4 Da Aka Sace Cikin Wata Tsohuwar Mota

Sojojin Rasha sun sheke dan jarida a Ukraine
Yanzu-Yanzu: Sojojin Rasha sun kashe wani fitaccen dan jaridar Amurka a Ukraine | Hoto: alarabiya.net
Asali: UGC

Wannan dai shi ne karon farko da aka samu rahoton mutuwar dan jaridar kasar waje da ke dauko rahoto daga yakin Rasha da Ukraine.

Hotuna suna yawo akan shafukan yanar gizo suna nuna katin shaidan Renaud da jaridar New York Times ta bashi.

Dan jaridar Amurka Juan Arredondo ya bayyana lokacin da sojojin Rasha suka kai masa hari tare da Brent Renaud a wani shingen bincike a Irpin na Ukraine, ranar Lahadi.

CBS News ta rahoto Juan na cewa::

"An harbe shi, an bar shi a wajen."

A wani labarin, Joe Biden, shugaban kasar Amurka ya nuna alamar wani yunkuri na kafa tarihi a kasuwancin crypto a Amurka da ma duniya baki daya, matakin da masana suka yi hasashen zai kawo sauyi a duniyar crypto.

Kara karanta wannan

Jirgin kasan Legas zuwa Ibadan ya tsaya tsakiyar daji saboda mai ya kare

An ce hakan zai kawo sauyi ne a cikin tsari mai tsawo da ake ta tsammani, wanda ya zama damuwa a duniyar crypto, yawanci saboda al'amurran da suka shafi ka'idojin kudi a duniya kasancewar ana ganin crypto a matsayin sabon nau'in kudi, a cewar wani rahoto na CNBC.

An samu labarin rashin fahimta a fadar shugabancin Amurka ta White House tsakanin jami'ai da sakatariyar baitulmalin kasar, Janet Yellen wanda hakan ya haifar da koma baya wajen tabbatar lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel