Ta Kacame: Mai Garkuwa Ya Yi Ƙorafi a Kotu, Ya Ce Abokansa Sun Cuce Shi Sun Bashi N200,000 Kacal Cikin N12m
- Wani Sado Ardo Bunkawu dan shekaru 28 da ake zargi da garkuwa da mutane ya roki alkali ya bi masa hakkinsa a wurin abokan harkarlarsa
- Ardo, bayan amsa laifin da ake tuhumarsa na garkuwa da mutane ya yi korafin cewa N200,000 kacal abokansa suka bashi cikin Naira miliyan 12 da suka karba
- Ya kuma kara da cewa N200,000 biyun ma bai yi sa'a ba a ranar domin dukkan kudin sun bata a yayin da ya ke hanzarin komawa gida
Yola - An sha dirama a kotu a Yola yayin da wani da ake zargi da garkuwa da mutane, Sadu Ardo Bunkawu, ya zargi abokin da sauran yan kungiyarsu ta garkuwa da zaluntarsa.
Ya bayyana hakan ne yayin da ake masa shari'a kan zargin hadin baki da garkuwa wanda sun saba wa sashi na 60 da 248(a) na Penal Code na jihar a kotun Majistare da ke Yola.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mohammed Abdulllahi Digil ne ke jagorantar zaman kotun kamar yadda Nigerian Tribune ta rahoto.
Ardo ya amsa laifinsa amma ya roki kotu ta kwato masa hakkinsa wurin abokan harkarsa
Da aka karanto masa tuhumar kuma aka fassara masa cikin harshen Fulfulde, wanda ake zargin ya amsa laifinsa.
Amma, ya ce:
"Ina son a yi min adalci kan rashin adalcin da sauran yan tawagar mu suka min. Sun bani N200,000 kacal cikin Naira miliyan 12 da muka karba na fansa."
Ardo, dan shekara 28 dan asalin kauyen Filingo, gundumar Gankiri a karamar hukumar Jada, Jihar Adamawa ya amsa cewa sun karbi kudin fansa N12m bayan sace Alhaji Umaru Diffawa da lhaji Umaru Babidi a nan garinsu.
Kason nawa N200,000 ma sun fadi garin sauri zuwa gida, Ardo
Ya bayyana cewa bai yi sa'a ba wannan ranar domin ya batar da kasonsa N200,000 garin saurin zuwa gida, rahoton Nigerian Tribune.
Ya yi bayanin cewa mutane bakwai cikin yan uwan wadanda suka yi garkuwa da su ne suka biya su kudin kuma bayan sun saki mutanen sai aka kira shi aka bashi N200,000 kacal.
Tunda farko, mai gabatar da kara ya shaidawa kotu cewa wanda aka yi karar sun hada baki da wasu mutane shida (ba bayyana sunansu ba) sun aikata laifin da aka gurfanar da shi a kai.
Bayan gurfanarwar, mai gabatar da karar ya roki kotu da dage zaman domin basu damar kammala bincike kuma su nemi shawara daga ofishin DPP.
Kotun ta amince ta dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 4 ga watan Afrilun 2022.
'Yan bindiga sun sace mutane 29 a wani ƙauyen Katsina, 'Yan Sanda
A wani rahoton, kun ji cewa mutane 29 ne yan bindiga suka sace yayin harin da suka kai kauyen Godiya a cewar rundunar yan sandan Jihar Katsina.
Mai magana da yawun rundunar a jihar, Gambo Isah, ya tabbatar da adadin mutanen yayin zantawa da Channels Television a ranar Talata.
Wasu gungun yan bindiga ne suka kai hari a Ruwan-Godiya a daren ranar Lahadi a karamar hukumar Faskari.
Asali: Legit.ng