Yan bindiga sun kashe manoma 2 sannan sun yi garkuwa da wasu mutane 4 a Sokoto

Yan bindiga sun kashe manoma 2 sannan sun yi garkuwa da wasu mutane 4 a Sokoto

  • Tsagerun yan bindiga sun hallaka manoma biyu a yayin da suke aiki a gonakinsu a garin Sardauna da ke karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto
  • Hakazalika maharan sun yi awon gaba da wasu mutum hudu a hanyar Sabon Birni-Goronyo a kwanaki hudu da suka gabata
  • Shugaban kungiyar yan banga a Sabon Birni, Musa Muhammad wanda aka fi sani da Blacky ya tabbatar da faruwar lamarin

Sokoto - Daily Trust ta rahoto cewa yan bindiga sun kashe wasu mutane biyu yayin da suke tsaka da aiki a gonakinsu a garin Sardauna da ke karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto.

An tattaro cewa an kashe manoman ne a ranar Lahadi, 6 ga watan Maris, da misalin karfe 3:30 na rana.

Yan bindiga sun kashe manoma 2 sannan sun yi garkuwa da wasu mutane 4 a Sokoto
Yan bindiga sun kashe manoma 2 sannan sun yi garkuwa da wasu mutane 4 a Sokoto Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Shugaban kungiyar yan banga a Sabon Birni, Musa Muhammad wanda aka fi sani da Blacky ya bayyana mamatan a matsayin Hamza Na’allah da Zubairu Haruna na yankin Sardauna da ke Sabon Birni.

Kara karanta wannan

Karar kwana: Kasa ta rufta da mutum 5 a garin taya abokinsu hakar kasar ginin aurensa

Blacky ya bayyana cewa su uku ne a lokacin da aka kai masu farmaki amma sai daya daga cikinsu ya tsere zuwa kauyen da ke kusa ba tare da ya ji rauni ba.

Maharan sun yi garkuwa da mutane 4

Ya ce duk da zaman lafiya da aka dan samu a yankin a yanzu, ana kai yan kananan hare-hare a kauyukan kakkara.

A cewarsa, maharan sun kuma sace mutane hudu a hanyar Sabon Birni-Goronyo a kwanaki hudu da suka gabata.

Sai dai, rahoton ya kawo cewa ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar yan sandan jihar Sokoto, ASP Sanusi Abubakar ba, domin tabbatar da lamarin.

Matasa sun fusata, sun damke yan bindiga biyu sun kona su kurmus

A wani labarin, wasu da ake zargin yan bindiga ne masu garkuwa da mutane sun rasa rayukansu a hannun mutane, kuma suka kona gawarsu ƙurmus a kauyen Anpam, karamar hukumar Mangu, jigar Filato.

Kara karanta wannan

Wahalar Mai: Annaru ta ci dan bunburutu da matarsa da sukayi ajiyan jarkokin mai a gida

Daily Trust ta rahoto cewa wasu fusatattun matasa ne suka halaka mutanen da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a yankin.

Rahoto ya nuna cewa kusan gidaje 13 mallakin Fulani fusatattun matasan suka ƙone a yankin bayan ƙashe mutanen biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng