Muhammad Sanusi II ya fadi yadda aka nemi a hana shi kafa bankin Musulunci a CBN

Muhammad Sanusi II ya fadi yadda aka nemi a hana shi kafa bankin Musulunci a CBN

  • Wata kungiyar Musulmai a Legas ta shirya taro inda Malam Muhammadu Sanusi II ya yi jawabi
  • Muhammadu Sanusi II ya bayyana kalubalen da suka fusakanta wajen kawo bankin Musulunci
  • Farfesa AbdulRazzaq Alaro yana cikin masu jawabi, yayi watsi da zargin musuluntar da Najeriya

Lagos - Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya na CBN, Muhammadu Sanusi II ya zargi wasu ‘yan Najeriya da yin amfani da addini wajen boye gaskiya.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Malam Muhammadu Sanusi II ya yi magana a kan wadanda suka nemi su yaki bankin musulunci da aka kafa a kasar nan.

Tsohon Sarkin na Kano ya yi jawabi ne a wajen wani babban taro da wata kungiya ta musulman ‘yan kasuwa suka shirya a jami’ar tarayya da ke garin Legas.

Kara karanta wannan

Rashin mai da rashin wuta: Ku cigaba da juriya, ai ba mulkin Buhari aka fara rashin ba: Femi Adesina

Sanusi II ya ce a lokacin da yake rike da CBN, ya yi kokarin nuna zargin da wasu ke yi na cewa ana shirin musuluntar da Najeriya ne, ya yi nesa da gaskiya.

Lamido Sanusi ya yi tayi wa al’umma bayanin irin amfanin wannan tsari na bankin musulunci, amma wasu suka ki gamsuwa saboda su na da sabanin addini.

Muhammad Sanusi II
Mai martaba Muhammadu Sanusi II Hoto: www.pulse.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar tsohon Sarkin, babban bankin CBN bai fasa cigaba da kawo tsarin bankin musulunci a Najeriya saboda kurum wasu 'yan daidaiku sun nuna adawarsu.

An ga canji a yau inji Sanusi II

Shekaru 10 da shigo da wannan tsari, Sanusi II ya ce an fara ganin sauyi, kuma babu abin da zai hana Najeriya zama cibiyar tsarin bankin musulunci a Afrika.

Daga baya an samu wadanda ba musulmai ba sun rungumi bankin Ja’iz. An rahoto Sanusi II yana cewa 40% na masu hannun jari a bankin, ba musulmai ba ne.

Kara karanta wannan

Shehu Sani: Idan da matan gwamnoni basu shilla kasar waje ba, da majalisa bata yi waje da kudurin mata ba

“Mun yi bakin kokarinmu wajen yin bayani. Idan mutane sun ki yarda, ba za mu fasa ba saboda su. Bayan shekaru 10, abubuwa sun canza zani.”
“Mu na da mutane da sun san gaskiya, ko kuma ba su san sanin gaskiya saboda su rika amfani da addini saboda wasu manufofinsu.” – Sanusi II.

Farfesa AbdulRazzaq Alaro wanda malamin shari’ar Musulunci ne a jami’ar Ilorin, ya yi jawabi a taron yana mai goyon bayan ra’ayin tsohon gwamnan na CBN.

Dalilin sauke Sanusi daga CBN

A makon da ya gabata, an ji Malam Muhammadu Sanusi II ya na bayanin abin da ya kai shi ga rasa kujerar gwamnan bankin CBN da kuma sarautar Kano.

Tsohon Sarkin Kano ya ce fadawa masu mulki gaskiya ne dalilin da ya sa aka sauke shi daga matsayinsa. Sanusi II ya bayyana haka ne a wajen wani taro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel