Hotunan 'ya'yan Buhari a wani taro tare da 'dan takarar shugabancin kasa

Hotunan 'ya'yan Buhari a wani taro tare da 'dan takarar shugabancin kasa

  • Dan takarar shugabancin kasa, Rochas Okorocha ya samu damar zantawa da 'ya'yan shugaban kasa Buhari a yayin wani taro
  • Sun hadu ne a wani taron da kungiyar mata 'yan jarida, NAWOJ ta shirya domin karrama Aisha Buhari tare da bata lambar yabo
  • Uwargidan shugaban kasan ta mika godiyarta ga kungiyar tare da sadaukar da lambar yabon ga duk 'yan Najeriya da ke cikin mawuyacin hali

Gagarumin taron karramawa da bayar da lambar yabo da kungiyar 'yan jarida mata ta Najeriya ta shirya a ranar Alhamis da ta gabata ya samu halartar manyan mutane a sassa daban-daban na fadin kasar nan.

An shirya wannan taron ne domin karrama nasarorin uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, wacce ta samu wakilcin 'ya'yanta mata, Halima Buhari-Sheriff da Zahra Buhari-Indimi.

Hotunan 'ya'yan Buhari a wani taro tare da 'dan takarar shugabancin kasa
Hotunan 'ya'yan Buhari a wani taro tare da 'dan takarar shugabancin kasa. Hoto daga Aisha Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

A yayin magana kan karramata da aka yi, uwargidan shugaban kasan ta yi wallafa a shafinta na Facebook kamar haka:

Kara karanta wannan

Matasan APC a arewa sun bayyana wanda suke so ya gaji Buhari daga kudu maso gabas

"Kungiyar 'yan jarida mata, NAWOJ ta karrama mi a yau da lambar yabon “Icon and Beacon of Hope for Empowerment.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"'Ya'yana mata biyu, Halima Buhari-Sheriff da Zahra Buhari-Indimi ne suka karba lambar yabon a madadina.
"Na sadaaukar da wannan lambar yabon ga dukkan 'yan Najeriya da ke cikin mawuyacin hali kuma ina mika godiyata ga wadanda suka bani wannan lambar yabon."

Daga cikin fitattun 'yan siyasa da suka ziyarci wurin taron, akwai Rochas Okorocha, tsohon gwamnan Imo wanda kuma dan takarar shugabancin kasa ne a karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da kuma ministan harkokin mata, Pauline Kedem Tallen.

A taron ne aka ga Okorocha tare da 'ya'yan shugaban kasan suna tattaunawa.

Bidiyon Rochas Okorocha ya na karanto ayar Qur'ani ya janyo cece-kuce

A wani labari na daban, bidiyon tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha yayin da ya ke karanto ayar Qur'ani yayin bayyana burinsa na tsayawa takarar shugabancin kasa ya bayyana.

Kara karanta wannan

Taron gangamin APC: Ana kyautata zaton Buhari zai zauna da gwamnoni domin dinke rikicin APC

Idan za mu tuna, Okorocha ya bayyana burinsa na tsayawa takarar shugabancin kasa a karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a wata wasika da ya aike wa shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan.

A yayin jawabinsa na bayyana burinsa, dan majalisar tarayyan an ga ya na karanto ayoyin Qur'ani yayin da ya ke bayyana cewa shi ne dan takarar da zai yi adalci, kamar yadda Allah yace a Suratul An-Nahl 16:90.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel