Bidiyon Rochas Okorocha ya na karanto ayar Qur'ani ya janyo cece-kuce

Bidiyon Rochas Okorocha ya na karanto ayar Qur'ani ya janyo cece-kuce

  • Bidiyon Sanata Rochas Okorocha ya na karanto ayar Qur'an, yayin da ya ke neman goyon bayan 'yan Najeriya da su zabe shi shugaban kasa ya bayyana
  • A cewar Okorocha, shi ne dan takara da zai iya yi wa 'yan Najeriya adalci kamar yadda Allah ya kira adalci a suratul An-Nahl a Qur'ani
  • Sai dai wannan karanto ayar ya janyo masa caccaka daga jama'a inda suka ce idanun 'yan Najeriya ya bude ba za a iya yaudararsu yanzu ba

Bidiyon tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha yayin da ya ke karanto ayar Qur'ani yayin bayyana burinsa na tsayawa takarar shugabancin kasa ya bayyana.

Idan za mu tuna, Okorocha ya bayyana burinsa na tsayawa takarar shugabancin kasa a karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a wata wasika da ya aike wa shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan.

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa za ta dauki mataki kan kudin karatun jami'a domin talaka ya samu ilmi

Bidiyon Rochas Okorocha ya na karanto ayar Qur'ani ya janyo cece-kuce
Bidiyon Rochas Okorocha ya na karanto ayar Qur'ani ya janyo cece-kuce. Hoto daga @realRochas
Asali: Twitter

A yayin jawabinsa na bayyana burinsa, dan majalisar tarayyan an ga ya na karanto ayoyin Qur'ani yayin da ya ke bayyana cewa shi ne dan takarar da zai yi adalci, kamar yadda Allah yace a Suratul An-Nahl 16:90.

Ya yi kira ga masu sauraren sa da su zabe shi saboda ya yi alkawarin samar da sabuwar Najeriya.

Okorocha wanda ke wakiltar mazabar Imo a majalisar dattawa ta 9, ya na daya daga cikin 'yan siyasa daga kudu maso gabas da suka shiga jerin masu son shugabancin kasa.

'Yan Najeriya sun yi martani

@Luter_O cewa ya yi: "Shin za ku bar wannan kyaftin din ya jagorance ku? Rochas ya iya nishadi."
@babaidris090 cewa yayi: "Don Allah ku jinjinawa Alhaji Rochas Okorocha wanda kwatsam ya zama Sheikh Alrochas bin Okorocha kafin zaben shugabancin kasa."

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Okorocha ya gana da Buhari kan kudirinsa na son zama magajinsa

@Aucho00 ya ce: "Ko da Rochas Okorocha na son shugabancin Najeriya??"
@Franklin_M_F ya ce: "Don Allah ku ba ni damar zama jagoranku a sabuwar Najeriya," Rochas Okorocha ya shafa gemunsa da yatsunsa, sannan ya bude idonsa tamkar wanda ke neman kiran aljanun da za su yi masa aiki kan wadanda ke sauraronsa."
@DareGlintstone ya ce: "Da karfi da yaji Rochas Okorocha ya kaoma Martin Luther King. Ba ni bane za ka jagoranta."
@bossmuhadan cewa yayi: "Don Allah wa ye ya bayar da umarnin bidiyon Rochas Okorocha ya na karanto ayar Qur'ani? Babu shakka tawagar kamfen din sa ce. Abun takaice, mutane idon su ya bude yanzu."
@iam_leochizzy ya ce: "Rochas ya ce shi ne Kyaftin Rochas kuma ya na son jagorantar Najeriya zuwa sabuwar makoma. Buhari ya yi mana alkawarin canji amma mun manta mu tambaye shi wanne irin canjin. Yanzu Rochas ya ce makoma, Don Allah Rochas wacce makoma muka dosa? Kafin ka kai mu inda bai dace ba."

Kara karanta wannan

Na kusa na yi wuff da ke idan Allah ya yarda – Lilin Baba ga Ummi Rahab

2023: Lokacin mulkin Ibo ya yi, Okorocha ya bayyana burinsa na shugabancin kasa

A wani labari na daban, tsohon gwamnan jihar Imo, kuma sanata mai wakiltar yankin Imo ta yamma, Rochas Okorocha, ya nuna kwadayinsa a kan tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Tsohon gwamnan, wanda yayi maganar yayin da wata kungiya wacce ta kira kanta da sunan 'Igbos for Rochas 2023 President', wato kungiya mai marawa Rochas bayan shugabancin kasa a 2023, wacce Jeff Nwaoha ya jagoranta, daga jihohi 5 na yankin kudu maso gabas, tace lokacin da kabilar Ibo za ta samar da shugaban kasar Najeriya yayi.

Okorocha ya lura duk sauran yankunan sun yi shugabancin kasa, amma banda kudu maso gabas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel