Da dumi-dumi: Buhari ya rattaba hannu kan sabuwar dokar zabe
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan sabuwar dokar zabe a ranar Juma’a, 25 ga watan Fabrairu
- An yi bikin rattaba hannu kan dokar da aka dade ana cece-kuce a kai a zauren majalisar fadar shugaban kasa da ke Abuja
- Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, da kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila duk sun hallara
Abuja – A karshe Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kan sabuwar dokar zabe.
An gudanar da wani biki na sanya hannu kan dokar a zauren majalisar zartarwa da ke fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Juma’a, 25 ga watan Fabrairu, jaridar The Cable ta rahoto.
Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila duk sun halarci taron.
Hakazalika shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi ma na cikin manyan mutanen da suka halarci bikin.
Ci gaban na zuwa ne wata guda bayan majalisar dokokin kasar ta gabatarwa shugaban kasar da dokar.
Da yake jawabi a taron, shugaban kasar ya bukaci 'yan majalisar da su hanzarta yin gyara ga sashe na 84 na dokar wanda ya tanadi haramtawa masu rike da mukaman gwamnati jefa kuri'a a zaben shugabannin jam'iyya ko kuma na 'yan takara, rahoton BBC Hausa.
Gwamnonin Jihohi za su sake sa kafar wando daya da ‘Yan Majalisa kan rigimar dokar zabe
A gefe guda, mun ji a baya cewa za a iya samun sabani tsakanin gwamnoni da ‘yan majalisar tarayya a dalilin wasu sharudodi biyu da aka cusa a cikin kudirin gyara dokar zabe.
Wani rahoto da Daily Trust ta fitar a ranar Laraba, 2 ga watan Fubrairu 2022 ya bayyana cewa sharudan da aka kawo za su iya sa a kuma yin watsi da kudirin.
A baya shugaba Muhammadu Buhari ya yi fatali da kudirin da ‘yan majalisa suka kawo da yake kokarin yin kwaskwarima ga dokar zaben da ake amfani da ita.
Asali: Legit.ng