Yakin Rasha da Ukraine: 'Yan majalisun Najeriya za su kwasho daliban Najeriya a Ukraine
- Majalisar wakilai a Najeriya ta ba da umarnin gaggauta kwashe 'yan Najeriya da ke karatu a kasar Ukraine
- Wannan na zuwa ne bayan da kasar Ukraine ta kaure da yaki tsakaninta da Ukraine a cikin 'yan kwanakin nan
- Majalisar ta ambaci wasu 'yan majalisun da za su tafi kasar Ukraine ranar Juma'a domin tabbatar da aikin
FCT, Abuja - Bayan barkewar yaki tsakanin kasashen Rasha da Ukraine, majalisar wakilai ta Najeriya ta bayyana cewa, za a yi mai yiwuwa domin tabbatar da kwashe dalibai 'yan Najeriya daga Ukraine.
Wannan na zuwa ne jim kadan bayan kasar Rasha ta kutsa kai cikin Ukraine tare da kai mummunan hari a wasu sansanonin sojin kasar, kamar yadda rahoton AlJazeera ya fada.
Majalisar ta ce, wasu jami'ai, ciki har da shugaban kwamitin harkokin waje na majalisa za su shilla kasar Ukraine domin tabbatar da kwaso daliban Najeriya.
Majalisar ta umarci shugaban majalisar, Alhassan Ado Doguwa (dan APC, daga Kano), shugaban kwamitin majalisar kan harkokin kasashen waje, Buba Yakub (dan APC, daga Adamawa) da su yi mai yiwuwa a lamarin.
Majalisar ta fadi haka ne yayin zamanta a yau Alhamis, inda ta fitar da sanarwar ta shafinta na Twitter.
Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin da Ahmed Munir (dan APC, daga Kaduna) ya gabatar a zauren majalisar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Da yake gabatar da kudirin, dan majalisar ya ce akwai bukatar Najeriya ta kwashe ‘yan kasarta daga Ukraine.
Munir ya ce rayukan ‘yan Najeriya na cikin hadari domin yakin na iya kara kamari cikin ‘yan kwanaki masu zuwa, wanda hakan zai iya jefa ‘yan Najeriya cikin mawuyacin hali.
Ya ce:
“Muna da adadi mai yawa na daliban da suke karatun digiri na farko da na biyu a halin yanzu a Ukraine wanda wani kaso daga cikin su suna karkashin tallafin karatu na gwamnati ne.
“Wannan kenan baya ga wasu jami’an diflomasiyyar Najeriya da iyalansu da ke ofishin jakadanci a Kiev da ‘yan Najeriya mazauna kasar Ukraine.
"Idan ba a samar da wani tsari na tsaro don samar da kariya ga 'yan kasarmu ba, za su iya makalewa ko kuma a cutar da su."
Wannan batu ne ya kai umarnin majalisa na gaggauta kwaso 'yan Najeriya daga Ukraine.
Duk wanda yayi mana shisshigi kan yakinmu da Ukraine zai fuskanci ukuba, Shugaban kasan Rasha
A wani labarin, shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, ya gargadi Amurka da sauran kasashen Turai su yi hattara kada su sa baki kan yakinsu da Ukraine a ko kuma su fuskanci mumunar ukuba.
Putin ya bayyana hakan ne da safiyar Alhamis yayinda yayi jawabi ga al'ummar kasar kan yanke shawarar kai hari Ukraine.
Yace:
"Shirye muke da duk sakamakon da zai biyo baya. Duk wanda yayi kokarin hana mu ko yayi mana barazana, al'ummarmu su sani cewa zasu mayar da martanin da ba'a taba gani ba.
Asali: Legit.ng