Wadanda Suka Sace Dagaci Da Mutum 14 Sun Rage Kudin Fansa, Yanzu Sun Ce a Basu Buhun Shinkafa 2 Da N4m

Wadanda Suka Sace Dagaci Da Mutum 14 Sun Rage Kudin Fansa, Yanzu Sun Ce a Basu Buhun Shinkafa 2 Da N4m

  • Wadanda suka yi garkuwa da dagacin kauyen Gwombe, Junaidu Danjuma da sauran ‘yan kauye 14 a wuraren Gwargwada da ke karamar hukumar Kuje a Abuje sun sauya bukatun su
  • Maimakon Naira miliyan 15 da suka bukata da farko a matsayin kudin fansa, sun zaftare inda suka koma Naira miliyan 4 da kuma buhunan shinkafa guda biyu
  • An samu rahotanni akan yadda aka sace ‘yan kauye 11 ciki har da matar mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na gundumar Gwargwada, Asabe Mohammed Koriya ranar 4 ga watan Fabrairu

Abuja - Masu garkuwa da mutanen da suka sace dan dagacin kauyen Gwombe, Junaidu Danjuma da sauran mutane 14 a yankin Gwargwada da ke karamar hukumar Kuje a Abuja sun sauya bukatun su, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bayan watanni 11, Iyalan yan kasuwa canjin Kano da DSS ta kama sun ga mazajensu

Yanzu sun koma bukatar Naira miliyan 4 da buhunan shinkafa 2 maimakon Naira miliyan 15 da suka bukata da farko.

Masu Garkuwa Sunyi Rangwamen Kudin Fansa, Yanzu Sun Ce a Basu Buhun Shinkafa 2 Da N4m
Masu Garkuwa Sunyi Rage Kudin Fansa, Yanzu Sun Ce a Basu Buhun Shinkafa 2 Da N4m. Hoto: Daily Trust
Asali: Depositphotos

Daily Trust ta ruwaito yadda suka sace mutanen kauyen guda 11 ciki har da matar mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na gundumar Gwargwada, Mrs Asabe Mohammed Koriya a ranar 4 ga watan Fabrairun 2022.

Sun harbe mutum daya a wurin bayan ya yi yunkurin tserewa

Washegari, masu garkuwa da mutanen sun koma wurinsa inda suka sace dan dagacin kauyen, Danjuma da wasu mutane biyu daban.

San harbe daya daga cikin su mai suna Kabiru Sani bayan ya yi yunkurin tserewa.

Wani dan ‘uwan wadanda aka sace wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya sanar da wakilin Majiyar Legit.ng ta wayar salula cewa a ranar Laraba masu garkuwa da mutanen suka zaftare kudin da suka bukata da farko, daga naira miliyan 15 zuwa 4 bayan mutane sun kammala ciniki.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Bama-baman' da yan bindiga suka ɗana sun tashi da rayukan dandazon Mutane a jihar Neja

A cewarsa, masu garkuwa da mutanen sun bukaci buhunhuna 2 na shinkafa, kayan shaye-shaye da katan din barasa.

Ya ce daya daga cikin wadanda aka sace ya tsere daga wurin su inda ya shaida wa ‘yan uwansu cwwa har yanzu suna hannun masu garkuwa da mutane.

‘Yan uwan wadanda aka sace suna ta neman taimako don hada kudin fansar ‘yan uwansu

Ya bukaci su tara naira miliyan 4 don a tura musu.

Kamar yadda ya ce:

“Yan uwan wadanda aka sace sunata yawo suna rokon jama’a akan su tara musu kudin fansa su kuma tara don siya musu buhunhunan shinkafa da kayan shaye-shayen.”

Mai girma Agabe din Gwargwada-Ugbada, Alhaji Hussaini Agabi Mam ya bayyana rashin jin dadin sa akan satar jama’an da ke ta aukuwa.

Ya bukaci jami’an tsaro da su kai dauki don a samu a sako wadanda aka sace.

Yayin da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan FCT, DSP Adeh Josephine, ta yi alkawarin tuntubar wakilin Daily Trust, amma har aka kammala rahoton bata ce komai ba.

Kara karanta wannan

Yan bindigar da suka sace kansila a Sokoto sun nemi a biya kudin fansa miliyan N60

'Yan bindiga sun sace babban limami da wasu mutane 10 yayin da suke sallah a Sokoto

A wani labarin, 'yan bindiga sun sace mutane 11 ciki har da babban limami, Aminu Garba, wanda ke shirin jagorantar mutane yin sallah Juma'a a jam'i a kauyen Gatawa da ke karamar hukumar Sabon Birni a Jihar Sokoto.

An sace limamin tare da wasu mutane uku ne a ranar Juma'a kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Maharan sun tare hanyar Sabon Birnin zuwa Gatawa a ranar Asaba, inda suka bindige mutane uku suka kuma sace wasu mutanen bakwai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164