MURIC ga 'yan Arewa kan kisan Hausawa a Abia: Ku yi hakuri, kada ku rama, ku barwa Allah

MURIC ga 'yan Arewa kan kisan Hausawa a Abia: Ku yi hakuri, kada ku rama, ku barwa Allah

  • Kungiyar MURIC ta roki yan arewa da su yi hakuri a kan kisan Hausawa da aka yi a kasuwar shanu da ke jihar Abia
  • Shugaban MURIC, Ishaq Akintola, ya ce kada yan arewa su ce za su yi ramuwar gayya, ya nemi su fawwalawa Allah lamarinsu kamar yadda suka saba yi
  • Ya jinjinawa dattako da kau da kai irin na mutanen arewa a duk lokacin da aka kashe masu mutane a kudancin kasar

Kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC) ta roki yan arewa a kan kada su rama kisan da aka yiwa wasu yan kasuwa yan arewa a jihar Abia.

Ishaq Akintola, daraktan MURIC, ya ce sun yi rokon ne don samun zaman lafiya a Najeriya, jaridar The Cable ta rahoto.

MURIC ga 'yan Arewa kan kisan Hausawa a Abia: Ku yi hakuri, kada ku rama, ku barwa Allah
MURIC ga 'yan Arewa kan kisan Hausawa a Abia: Ku yi hakuri, kada ku rama, ku barwa Allah Hoto: The Guardian
Asali: Facebook

Da farko mun ji yadda yan bindiga suka kashe mutane da dama a wani hari da suka kai sabuwar kasuwar shanu a garin Omumauzor da ke karamar hukumar Ukwa ta yamma da ke jihar.

Kara karanta wannan

Shiga tashin hankali: Abba Kyari da jiga-jigai 6 da suka fada rashin lafiya yayin bincikarsu

A cikin wata sanarwa a ranar Laraba, 23 ga watan Fabrairu, Akintola ya ce babu wanda ke da ikon daukar ran wani, inda ya ce an kai harin Abia ne domin tunzura yan arewa zuwa ga ramuwar gayya, rahoton Daily Post.

Akintola ya ce:

“Kimanin yan kasuwa yan arewa 15 da shanayensu 150 aka kashe a jihar Abia a makon da ya gabata.
“Koda dai mun san cewa wannan ba shine karo na farko da irin haka ke faruwa a kudu maso gabashin Najeriya ba, muna rokon yan arewa da kada su rama. Babban dalilin rokonmu shine don ganin zaman lafiya ya wanzu a kasar a daidai wannan lokaci da muke gangara zuwa karshen gwamnatin Muhammadu Buhari.
“MURIC ta yi Allah-wadai da kisan da ya afku a Abiya a makon jiya. Shakka babu, mun yi Allah wadai da dukka kashe-kashen da kuma ayyukan ta’addanci walau na makiyaya, ko mayakan kabilanci ko masu neman ballewa. Rayuwa mai tsarki ce kuma babu wani dan adam da ke da hakkin ya dauki ran wani ba bisa ka'ida ba.

Kara karanta wannan

NDLEA ta cafke kudi har $4.7 na jabu a Abuja, ta yi ram da maijego dauke da kwayoyi

“Muna umartan yan arewa da su ci gaba da hakuri da bin doka. Wannan hari musamman na Abia an yi shi ne domin tunzura yan arewa zuwa ga rabuwa wanda ka iya haddasa sabon rikici na yakin basasa. Kada arewa ta ma tauna tsakuwa balle a kai ga hadiye shi."

Yan arewa su kara hakuri

Akintola ya yaba ma yan arewa akan hakurin da suka yi.

Ya ce:

“Arewa yana hadiye fushinsa a duk lokacin da yan kudu suka kashe masa mutanensa, ko razana su ko kuma tozarta su. Bayanan mun nuna cewa hakan ya faru lokuta da dama musamman a shekaru bakwai da suka gabata ba tare da arewa ya yi yunkurin ramawa ko sau da yaba. Muna jinjinawa matasa da dattawan arewa sannan muna bukatarsu da su yi hakuri sannan su ci gaba da nuna halin girma.
“Muna jimamin duk wadanda suka rasa rayukansu sakamakon kashe-kashen da ake yi a fadin kasar nan, muna kuma addu’ar Allah ya baiwa iyalansu hakurin jure rashin. Muna kuma addu’ar samun dawwamammen zaman lafiya, kwanciyar hankali a siyasa gami da bunkasar tattalin arziki a kasarmu ta Najeriya.”

Kara karanta wannan

An damke wani jami'in dan sandan bogi mai amfani da kayan sarki yana damfarar mutane

Kisan Hausawa dillalan shanu a Kudu: Kungiyoyin Arewa sun fusata, sun tura gargadi ga gwamnatin Abia

A baya mun ji cewa Gamayyar kungiyoyin arewa (CNG) da na matasan arewa (AYCF) sun yi Allah wadai da harin da aka kai kan yan arewa a kasuwar shanu da ke jihar Abia wanda ya yi sanadiyar rasa rayuka, sun ce ba za a lamunci hakan ba.

Yan bindiga sun farmaki sabuwar kasuwar shanu da ke garin Omumauzor, karamar hukumar Ukwa ta yamma a jihar Abia a ranar Talata, 15 ga watan Fabrairu, da misalin 11:35 na dare, inda suka kashe mutane takwas.

Yayin da suke martani ga harin a sanarwa daban-daban, kungiyoyin sun yi watsi da lamarin sannan sun yi kira ga gwamnatin jihar Abia da ta hukunta wadanda suka aikata ta’asar, Daily Trust ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng