Rikicin Hijab a Kwara: Iyalan wanda aka kashe sun nemi a biya su diyyar N113m

Rikicin Hijab a Kwara: Iyalan wanda aka kashe sun nemi a biya su diyyar N113m

  • Yan uwan dalibin da aka kashe a lokacin rikicin Hijabi a makarantar Oyun Baptist High School, Ijagbo da wasu Musulmai a jihar Kwara sun nemi gwamnatin jihar ta biya diyyan N113, 388,000
  • Iyalan dai sun mayarwa gwamnati da naira miliyan daya da ta fara basu a yayin wata ganawa da gwamnatin jihar, Farfesa Mamman Jibril
  • Hakazalika wadanda suka jikkata a harin sun mayar da N250,000 da aka baiwa kowannensu

Kwara - Iyalan Habeeb Idris wanda aka kashe a lokacin rikicin Hijabi a makarantar Oyun Baptist High School, Ijagbo da wasu Musulmai a jihar Kwara sun nemi N113, 388,000 a matsayin diyyah daga gwamnatin jihar.

Da farko Musulman da iyalan sun mayar da naira miliyan daya da gwamnati ta baiwa iyayen marigayin a lokacin wata ganawa da sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Mamman Jibril, Daily Trust ta rahoto

Kara karanta wannan

Kusoshin Gwamnati za su amsa tambayoyi a Majalisa kan zargin cuwa-cuwar albashi

Hakazalika Musulmai 11 da aka jiwa munanan raunuka a yayin harin suma sun dawo da N250,000 da gwamnatin jihar Kwara ta basu ta hannun Abdullahi Abubakar da Taofeeq Mustafa (wanda abun ya ritsa da shi) a madadin al’umman Musulmai na Offa/Oyun.

Rikicin Hijab a Kwara: Iyalan wanda aka kashe sun nemi a biya su diyyar N113m
Rikicin Hijab a Kwara: Iyalan wanda aka kashe sun nemi a biya su diyyar N113m Hoto: Kwara
Asali: Twitter

Da yake jawabi ga manema labarai a Ilorin, babbar birnin jihar a ranar Litinin, shugaban kungiyar matasan Musulmai na Kwara, Ustaz Abdurrazzaq, ya kuma bukaci gwamnatin jihar da ta bayar da diyya mai kauri ga Musulmai 11 da suka ji mummunan rauni a yayin rikicin hijabi na Ijagbo.

A cewarsa, ya kamata gwamnati ta dauki cikakken alhaki na biyan kudin asibiti da duk wasu dawainiya na Musulman da aka jikkata a yayin rikicin, rahoton Leadership.

Ya ce:

“Ya kamata gwamnati ta guji kiran makarantun gwamnati a matsayin na mishan a cikin jawabanta.

Kara karanta wannan

Zamfara: Majalisa ta sake aike wa da zazzafan sako ga mataimakin Matawalle kan batun tsige shi

“Wannan gagarumin cin fuska ne ga hukunce-hukuncen kotuna. A idon doka, babu wani abu mai kama da makarantun mishan a jihar Kwara.
“A hukunta hukumomin makarantar sakandare ta Oyun Baptist, Ijagbo, wadanda suka ki aiwatar da hukunce-hukuncen kotuna da umurnin gwamnati kan amfani da hijabi da kuma yin biyayya ga CAN maimakon wacce ta dauke ta aiki; Gwamnatin jihar Kwara.”

Al-Amin ya kuma bukaci a dakatar da shirin sake bude makarantar na Baptist da ke Ijagbo, domin gudanar da taron Baptist mai zuwa, ya kara da cewa;

"Wannan rashin hankali na gwamnatin jihar Kwara zai zama tamkar rawa a kan kabarin marigayi Habeeb Idris."

Domin zama mafita ga rikicin da yaki ci yaki cinyewa, shugaban matasan Musulmai ya nemi a aiwatar da hukunce-hukuncen babbar kotun jihar Kwara da kotun daukaka kara kan lamarin.

Lauya mai kare Musulman Ijagbo kan lamarin, Ibrahim Akaje, ya fada ma jaridar Daily Trust cewa abun mamaki shine babu wanda yan sanda suka kama tun bayan da aka kai rahoton lamarin.

Kara karanta wannan

El-Rufai ya cika shekaru 62 a duniya, gwamnonin APC sun aike masa da sako

Da aka tuntube shi, babban mai ba gwamnatin jihar Kwara shawara kan harkokin addini, Ibrahim Dan Megoro ya ki cewa uffan a kan lamarin.

Rikici kan sanya Hijabi a Kwara: MURIC ta fusata, ta zargi 'yan sanda da sanya wajen bincike

A baya mun kawo cewa daraktan kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC), Farfesa Ishaq Akintola, ya zargi rundunar yan sanda da yin sanya kan batun kisan wani dalibi, Habeeb Idris, na makarantar Baptist, Ijagbo da ke karamar hukumar Oyun ta jihar Kwara.

An tattaro cewa an harbe dalibin ne a ranar Alhamis, a yayin gudanar da zanga-zanga kan hijabi. An kuma ce wasu dalibai hudu sun jikkata a lamarin.

Akintola ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, 6 ga watan Fabrairu, jaridar Vanguard ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng