Yan bindiga sun yi garkuwa da kansila da wasu mutane 8 a Sokoto

Yan bindiga sun yi garkuwa da kansila da wasu mutane 8 a Sokoto

  • Yan bindiga sun kai hari kauyen Yar Tsakuwa a karamar hukumar Rabah da ke jihar Sokoto, sun yi awon gaba da wani kansila mai ci, Lawali Bello
  • Maharan sun kuma sace diyar wani tsohon kansila da suka zo taron suna yankin da wasu da dama
  • Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa yan bindigar sun yashe gidajensu da shagunansu inda suka kwashi babura, kayan abinci da magunguna daban-daban

Sokoto - Yan bindiga sun farmaki kauyen Yar Tsakuwa a karamar hukumar Rabah da ke jihar Sokoto, sun yi garkuwa da mutane tara, cikinsu harda wani kansila mai ci, Lawali Bello wanda aka fi sani da LBY.

Diyar wani tsohon kansila da ke yankin, Alhaji Abdullahi Garba, na cikin wadanda aka sace, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kaduna: Ina shirin aurar da 2 daga cikin 'ya'yana mata da aka sace, Basarake

Yan bindiga sun yi garkuwa da kansila da wasu mutane 8 a Sokoto
Yan bindiga sun yi garkuwa da kansila da wasu mutane 8 a Sokoto Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wani mazaunin yankin, Nazifi Abdullahi, ta fadawa jaridar Daily Trust cewa yan bindigar sun shigo da safiyar Asabar sannan suka yi ta aiki har zuwa 2:50 na tsakar dare.

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Sun yashe dukka gidajenmu da shaguna, ciki harda shagunan magani.”

Ya kuma kara da cewar maharan sun sace Babura masu yawa, kayan abinci da magunguna iri-iri.

Ya bayyana cewa da farko miyagun dun sace mutane 20 amma sai suka saki wasunsu a hanyarsu ta fita daga kauyen.

Abdullahi ya ce:

“A yanzu mutane tara na a hannunsu, ciki harda wani kansila mai ci da matansa da kuma diyar tsohon kansilanmu.”

Ya bayyana cewa mata da diyar tsohon kansilar sun zo kauyen ne domin halartan wani taron suna na jikansu, domin tun dama sun bar kauyen sakamakon hare-haren rashin imani da yan bindiga ke kaiwa.

Kara karanta wannan

An damke wani jami'in dan sandan bogi mai amfani da kayan sarki yana damfarar mutane

Abdullahi ya kara da cewa an dauki mutum daya da yan bindigar suka harba zuwa babban asibitin Talata Mafara a jihar Zamfara domin jinya.

Zuwa yanzu, ba a samu jin ta bakin kakakin yan sandan jihar Sokoto, ASP Sanusi Abubakar ba, rahoton Independent.

An kuma: 'Yan ta'adda sun kai farmaki Zamfara, sun sheke rayuka 18

A wani labarin kuma, mun ji cewa a kalla rayuka 18 ne suka salwanta yayin da wasu masu yawa suka raunata bayan farmakin 'yan ta'adda a Kadaddaba da ke karamar hukumar Anka ta jihar Zamfara.

Premium Times ta ruwaito cewa, farmakin ya kwashe kusan sa'o'i hudu tunda 'yan ta'addan sun bayyana wurin karfe goma na dare ne kuma suka kai har hudun asuba kuma shi ne na farko da aka taba kai wa kauyen.

Kilomita kadan ke tsakanin kauyen Kadaddaba da kwalejin gwamnatin tarayya ta Anka, wacce ba ta da nisa da garin Anka.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai farmaki gidan sarkin Hausawa a yankin Kaduna, sun sace mata da yara mata 4

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng