Rashin tsaro: Gwamnatin Katsina ta haramta kungiyar Yan-Sa-Kai a fadin jihar
- Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya haramta kungiyar Yan-sa-kai a fadin jihar
- Gwamnatin Katsina ta ce ta dauki wannan mataki ne saboda ayyukan laifi da yan kungiyar ke aikatawa na kisan ganganci da kuma sace-sace
- Mai ba gwamnan shawara na musamman kan harkokin tsaro, Ibrahim Katsina, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar
Gwamnatin jihar Katsina a ranar Litinin, 14 ga watan Fabrairu, ta sanar da haramta kungiyar Yan-sa-kai a jihar, jaridar Punch ta rahoto.
Gwamnatin ta bayyana cewa ta dauki matakin ne saboda yawan laifukan da mambobin kungiyar ke aikatawa.
Kungiyar na dauke ne da mutanen da suka sadaukar da kansu domin taimakawa a lamuran tsaro.
Wani jawabi daga mai ba Gwamna Aminu Masari shawara na musamman kan harkokin tsaro, Ibrahim Katsina, ya yi zargin cewa wasu yan kungiyar suna aikata kisa ba tare da shari’a ba da kuma sace-sace.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sanarwar ta fayyace cewa kungiyoyin yan banga wadanda mambobinsu ke aiki a karkashin hukumar yan sanda ne kadai gwamnatin jihar ta sani, rahoton BBC Hausa.
Sanarwar ta ce:
“Gwamnatin jihar Katsina ta haramta ayyukan ’Yan Sa Kai, saboda yadda kungiyar ta yi kaurin suna wajen aikata laifuka a jihar, wanda a kodayaushe ke kai ga kisan bayin Allah da basu ji ba basu gani ba, tare da wawure dukiyoyinsu.
“Gwamnatin jihar Katsina ta amince da ayyukan kungiyar ‘yan banga da ke karkashin kulawar hukumar ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro da masarautun gargajiya ne kawai.
“Daga yanzu, a dunga mika wadanda ake zargi ga yan sanda ko wani hukumar tsaro don yin bincike da kyau da daukar matakin da ya kamata. Kada wanda ya dauki doka a hannunsa."
Yan bindiga sun yi awon gaba da jami’in kwastam a jihar Zamfara, sun nemi a biya N10m
A wani labari na daban, mun ji cewa yan bindigar da suka addabi al’umman karamar hukumar Tsafe da ke jihar Zamfara sun yi garkuwa da wani jami’in kwastam da wasu mata shida, HumAngle ta rahoto.
An yi garkuwa da jami’in kwastam din mai kula da jihohin Kano da Jigawa, Muhammad Hassan Lawal wanda ya ziyarci iyalinsa a daren ranar Juma’a, 11 ga watan Fabrairu.
A cewar Hassan Tsafe, wani mazaunin kauyen da abun ya faru kan idon sa, maharan sun shafe kimanin mintuna 30 kafin sojojin da aka kira suka iso.
Asali: Legit.ng