Innalillahi: 'Yan bindiga sun sace matar mataimakin shugaban PDP, da wasu mutum 10 a Abuja
- Wasu masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da mutane 11 a wani yankin babban birnin tarayya Abuja
- Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, daga cikin wadanda aka sacen, akwai matar mataimakin shugaban PDP na wani yanki
- Lamarin ya jawo tashin hankali, yayin da 'yan bindigan suka nemi dangin su biya makudan kudade kafin su sako mutanen 11
Kuje, Abuja - Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Mrs Asabe Mohammed Koriya, matar mataimakin shugaban jam’iyyar PDP a gundumar Gwargwada a karamar hukumar Kuje a Abuja. An sace ta ne tare da wasu mutane 10.
Dan uwan daya daga cikin wadanda abin ya shafa Salihu Ibrahim ya ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a da misalin karfe 5 na yamma a mahadar Gwargwada-Gwombe daura da unguwar Rubochi.
Ya ce wadanda abin ya shafa na komawa kauyukan Gwombe da Pesu ne bayan sun halarci wani taron siyasa a kauyen Gwargwada da ke makwabtaka da su, inji rahoton Daily Trust.
Ya ce ‘yan bindigar wadanda adadinsu ya haura 30 kuma dauke da bindigu, sun tare titin da itace. Sun buga baburansu tare da yin awon gaba da wadanda abin ya shafa cikin daji.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewarsa:
“Amma wasu mutane biyu da ke kan babur sun tsere. Da ganin masu garkuwa da mutane sai suka jefar da babur din suka gudu cikin daji amma masu garkuwar sun banka ma babur din wuta."
Agabe na Gwargwada-Ugbada, Alhaji Hussaini Agabi Mam, ya tabbatar da sace mutane 11 da suka hada da matar shugaban jam’iyyar PDP na yankin.
A kalamansa:
“Uku daga cikin wadanda abin ya shafa sun fito daga garina, hudu daga Pesu yayin da sauran wadanda abin ya shafa ‘yan kauyen Gwambe ne da ke makwabtaka da su."
An ce wadanda suka yi garkuwa da su sun bukaci a biya su Naira miliyan 25 kafin su sako mutanen 11.
Sarkin ya tabbatar da haka ne ga manema labarai a fadarsa a jiya, inda ya ce masu garkuwan sun kira waya da misalin karfe 9 na safiyar ranar Litinin domin sanar da su cewa wadanda suka sacen suna hannunsu.
Sarkin ya kara da cewa wani dan uwan daya daga cikin wadanda abin ya shafa ya shaida wa masu garkuwa da mutanen cewa babu wani daga cikin wadanda abin ya shafa da zai iya biyan Naira 100,000 kafin a zo ga Naira miliyan daya ba.
Ya ce tun daga lokacin ne masu garkuwa da mutanen suka daina daukar waya.
Sai dai mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, DSP Adeh Josephine, bata mayar da martani ga sakon wayar salula da aka aike mata kan lamarin ba.
'Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon kakakin majalisa, Duruji
Masu garkuwa da mutane sun sace tsohon kakakin majalisar jihar Imo, Lawman Duruji, kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Wakilin Punch ya tattaro bayanai akan yadda aka sace Duruji a karamar hukumar Ehime Mbano ranar Asabar a Oriagu yayin da ya ke dawowa daga wani taro.
Sun kuma yi garkuwa da wani dan kasuwa a Owerri, wanda aka fi sani da Ezzybee.
Har ila yau, an sace matar wani tsohon shugaban karamar hukumar Okigwe, Frank Onwunere.
Sannan an sace wasu a daidai Okwelle da ke karamar hukumar Onuimo a cikin jihar da kuma wasu a Umbomiti da ke Mbaitili da Amaraku a karamar hukumar Mbano da ke cikin jihar.
Kaduna: Jami'an tsaro sun ragargaji 'yan bindiga, sun kubutar da wadanda aka sace
A wani labarin, jami’an tsaro sun kubutar da wasu mutane bakwai da aka yi garkuwa da su daga hannun ‘yan bindiga da suka kai farmaki Ungwan Garama, da ke yankin Maraban Rido Janar na karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna.
An tattaro daga majiyoyi cewa an samu kiran aukuwar tashin hankali daga yankin inda jami’an tsaro suka yi gaggawar kai daukin dakile ‘yan bindigan, Daily Trust ta ruwaito.
Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro na cikin gida a jihar Kaduna ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce karfin wutar da sojojin suka yi ya tilasta wa 'yan ta'addan tserewa.
Asali: Legit.ng