Tsige mataimakin gwamnan Zamfara: Majalisa ta lissafo laifukan Aliyu Gusau
- Maajalisar jihar Zamfara ta yi yunkurin tsige mataimakin gwamnan jihar, Mahadi Aliyu Gusau saboda wasu dalilai
- Bayan da aka yi ta dambarwa kan batun tsige mataimakin gwamnan, ya garzaya kotu domin kare kansa
- Sai dai, majalisar ta fitar da sanarwar da ta bayyana irin laifukan da mataimakin gwamnan ya yi har ake son tsige shi
Jihar Zamfara - Majalisar dokokin jihar Zamfara ta bai wa mataimakin gwamnan jihar Mahadi Ali takardar tsige shi, inji rahoton Premium Times.
Hakan ya zo ne a ranar Litinin, kwanaki uku bayan da majalisar ta samu bukatar fara shirin tsige shi.
A baya an tattaro cewa, an ruwaito yadda Majalisar ta fara wani sabon yunkuri na tsige mataimakin gwamnan, Aliyu Gusau.
Mataimakin kakakin majalisar, Musa Bawa, a zaman majalisar na ranar Juma’a, ya mika takardar neman a tsige mataimakin gwamnan.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mista Bawa, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin majalisar kan asusun gwamnati, ya gabatar da kudirin a duba bukatar tsige Gusau.
Abin da ya faru tun farko
Mataimakin gwamnan ya raba gari da gwamna Bello Matatwalle ne bayan da ya ki shiga jam'iyyar APC tare da a bara.
Dukkansu sun hau mulki ne a jam’iyyar PDP bayan da kotun koli ta haramtawa ‘yan takarar jam’iyyar APC sakamakon zaben 2019.
Sanarwa na tsigewa ga Gusau
Majalisar a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Shamsudeen Basko, shugaban kwamitin riko na majalisar, yanzu haka ta tattauna da mataimakin gwamnan ta hannun sakataren gwamnatin jihar.
Premium Times ta rahoto Mista Basko yana cewa:
“Bayan cika sharuddan sashe na 188 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima) wanda ya bukaci 1/3 na daukacin ‘yan majalisa su amince da sanarwar tsige shi.
“Majalisar karkashin jagorancin Rt. Hon. Shugaban majalisar ya amince da wannan sanarwar ta yadda ya dace kuma bisa tanadin doka."
Mista Basko ya ce a 2021 majalisar ta gayyaci mataimakin gwamnan da ya gurfana a gabanta, sai ya ki amsa gayyatar da aka yi masa, a maimakon haka ya garzaya kotu, alhali ba su da niyyar tsige shi a lokacin kamar yadda ake zargi.
A cewar dan majalisar, majalisar ta bi hukuncin da kotun ta yanke.
Laifukan Aliyu Gusau
A cikin sanarwar, Mista Basko ya ce ana zargin mataimakin gwamnan ne da laifin yin amfani da mukaminsa, da wadata kansa da aikata laifuka ta hanyar amfani da kudaden jama'a da kuma gazawa wajen gudanar da ayyukan gwamnati.
Ya ce:
“Amfani da ofishinsa. Wannan ya hada da saba wa kundin tsarin mulki sashe na 190 da na 193 (1), (2) (a) (b) (c), na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya 1999 (wanda aka yi masa kwaskwarima).
“Masu aikata laifuka ta hanyar amfani da kudaden jama’a; ya hada da karkatar da kudaden gwamnati da aikata laifuka, da hada baki da zamba a jihar da kuma amincewa da yin murabus na rashin tabbas a ofishinsa.
"Rashin sauke ayyukan tsarin mulki wanda ke haifar da rashin biyayya."
Kokarin jin ra’ayin mataimakin gwamnan ya ci tura domin an kasa samunsa ta sakataren yada labaransa, Babangida Zurmi.
Majalisar dokokin jihar Zamfara ta musanta shirin tsige mataimakin gwamna
A wani labarin, Majalisar dokokin Zamfara ta musanta cewa tana shirin tsige mataimakin gwamnan jihar, Mahdi Aliyu Gusau.
Television Continental ta ruwaito cewa ‘yan majalisar sun ce mataimakin gwamnan kawai suke so ya bayyana a gaban majalisar sannnan ya kuma amsa wasu tambayoyi.
'Yan majalisar suna zargin Gusau da rashin da'a a hukumance da kuma shirya taron siyasa lokacin da jihar ke juyayin mutuwar mutane hamsin da shida da' yan bindiga suka kashe a karamar hukumar Maradun ta jihar.
Asali: Legit.ng