2023: Lokacin mulkin Ibo ya yi, Okorocha ya bayyana burinsa na shugabancin kasa

2023: Lokacin mulkin Ibo ya yi, Okorocha ya bayyana burinsa na shugabancin kasa

- Tsohon gwamna jihar Imo, kuma sanata, Rochas Okorocha, yana da burin zama shugaban kasar Najeriya a 2023

- Ya sanar da hakan ne bayan wasu taron magoya bayansa sun kai masa ziyara, kuma yayi na'am da su

- A cewarsa, 'yan kabilar Ibo suna da son zaman lafiya a duk inda suka tsinci kansu, suna neman hadin kan kowa

Tsohon gwamnan jihar Imo, kuma sanata mai wakiltar yankin Imo ta yamma, Rochas Okorocha, ya nuna kwadayinsa a kan tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Tsohon gwamnan, wanda yayi maganar yayin da wata kungiya wacce ta kira kanta da sunan 'Igbos for Rochas 2023 President', wato kungiya mai marawa Rochas bayan shugabancin kasa a 2023, wacce Jeff Nwaoha ya jagoranta, daga jihohi 5 na yankin kudu maso gabas, tace lokacin da kabilar Ibo za ta samar da shugaban kasar Najeriya yayi.

Okorocha ya lura duk sauran yankunan sun yi shugabancin kasa, amma banda kudu maso gabas.

A cewarsa; "Ina matukar farinciki da ku ka ga cancanta ta. Kuma nayi farincikin yadda ku ka ajiye harkokinku ku ka kama hanya mai nisa, ku ka zo har inda nake don mara min baya akan fitowa takarar shugabancin kasa.

"Na duba kokarinku. Ku ka ce lallai kuna bukatar in tsaya takarar shugabancin kasa, na ji dadi kwarai.

KU KARANTA: An gwangwaje mutumin da yayi wa Buhari tattaki da kyautar mota da makuden kudi

2023: Lokacin mulkin Ibo yayi, Okorocha ya yi jirwaye mai kama da wanka
2023: Lokacin mulkin Ibo yayi, Okorocha ya yi jirwaye mai kama da wanka. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

"Wajibi ne a gareni in jinijina muku a kan yadda ku ka saki komai, ku ka taho gareni.

"Hakika an dade ana yi wa 'yan kabilar Ibo fassara mara kyau, amma Ibo sun fi kowa son zaman lafiya a Najeriya, kuma duk inda ka gansu, za ka ga suna iyakar kokarin ganin sun samar da cigaba da zaman lafiya.

KU KARANTA: Hotunan motocin alfarma da Regina Daniels take hawa tun bayan aurenta da Ned Nwoko

"Zallar Ibo ba za su iya samar da shugaban kasa ba a kasar nan, muna bukatar hadin kan Hausawa, Yarabawa da sauran yankuna, kafin mu cimma gaci."

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya roki gwamnatin tarayya da ta taimaka ta gina tashar jirgin sama a jiharsa kuma ta fadada kogin Neja har zuwa Lokoja, don bubbugo da tattalin arzikin jihar da Najeriya gabadaya.

Ya bayyana wa manema labaran cikin fadar shugaban kasa hakan a ranar Talata, bayan taron da suka yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel