Zamfara: Ƴan bindiga sun kashe mutum 33 saboda ƙin biyan harajin N40m da suka saka a wasu ƙauyuka
- Majiyoyi sun bayyana yadda ‘yan bindiga suka kai farmaki Nasarawar Mai Fara da ke karamar hukumar Tsafe bayan gaza biyan harajin N40m da suka kallafa musu
- 'Yan bindigan sun halaka fiye da mutane 30 yayin da suka yi garkuwa da fiye da mutane 30 kuma yawanci mata ne a ranar Juma’a da rana bayan kai hare-hare daban-daban
- Sun kai harin garin Nasarawar Mai Fara da ke karamar hukumar Tsafe, Yar Katsina da ke karamar hukumar Bungudu da kauyen Nasarawa da ke karamar hukumar Bakura
Zamfara - ‘Yan bindiga sun halaka fiye da mutane 30, sannan sun yi garkuwa da wasu wadanda yawanci mata ne sakamakon hare-hare daban-daban a ranar Juma’a cikin Jihar Zamfara, Premium Times ta ruwaito.
Sun kai harin ne kauyen Nasarawar Mai Fara da ke karamar hukumar Tsafe, Yar Katsina da ke karamar hukumar Bungudu da kauyen Nasarawa da ke karamar hukumar Bakura.
Tun shekarar 2021 hare-hare suka yawaita a yankin. Majiyoyi daban-daban sun shaida wa Premium Times cewa sun kai harin Nasarawar Mai Fara ne saboda mazauna yankin sun gaza biyan harajin N40m da suka kallafa musu.
Wani shu’umin dan bindiga, Ada Aleru ne ya ke jagorantar ta’addanci a yankin da wuraren Faskari da ke Jihar Katsina.
Abubakar Bala, mazaunin Tsafe ya ce sun kai harin da ya shafi fiye da mutane 20 wadanda suka rasa rayukansu a ranar Juma’a da yamma.
Sun halaka babban limamin yankin
A Bakura kuwa, wani ma’akacin asibiti, Masud Kyambarawa ya sanar da Premium Times cewa sun halaka mutane uku a yankin ciki har da babban limamin yankin, Akilu Dan Malam.
Kamar yadda ya shaida:
“Jiya ina garin na ji ana harbe-harbe. Daga nan muka gudu wani kauye da ke makwabtaka da garin a Rabah, Jihar Sokoto. Gaskiya mummunan lamari ne.
“Musamman yara da mata sai gudu suke yi dajika don tsira. Alhamdulillah mun dawo lafiya amma mun ji labarin yadda mutane 3 suka rasu.”
A kauyen Yar Katsina da ke Bungudu kuwa, ‘yan bindiga sai da suka hana mutane zuwa sallar Juma’a.
Yanzu haka dai an tsinci gawawwaki 10 na jama’a a kauyen Yar Katsina
Abdul Balarabe, wani karamin dan jarida da ke Gusau ya ce akalla mutane 10 ne suka rasu sakamakon harin amma har yanzu akwai wadanda ba a gani ba, akwai yuwuwar garkuwa da su aka yi.
Bala ya kara da cewa:
“An ga gawawwaki 10 kuma har yanzu akwai wadanda ba a gani ba. Mazauna yankin sun ce ba su tabbatar ko garkuwa da su aka yi ba ko kuma boyewa su ka yi ba. ‘Yan bindiga sun shiga kauyen ne lokacin sallar Juma’a.”
Bala ya koka akan hare-haren da ke kara yawa a titin Funtua zuwa Gusau.
A cewarsa:
“Akwai hatsari bin hanyar Sheme zuwa Yankara da wuraren Kucheri, kafin a isa Tsafe.”
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Mohammed Shehu, ya yi alkawarin tabbatar da labarai sannan ya tuntubi wakilin Premium Times amma har lokacin rubuta wannan rahoton bai yi hakan ba.
Yan bindiga sun sace mutane 29 a wani ƙauyen Katsina, 'Yan Sanda
A wani rahoton, kun ji cewa mutane 29 ne yan bindiga suka sace yayin harin da suka kai kauyen Godiya a cewar rundunar yan sandan Jihar Katsina.
Mai magana da yawun rundunar a jihar, Gambo Isah, ya tabbatar da adadin mutanen yayin zantawa da Channels Television a ranar Talata.
Wasu gungun yan bindiga ne suka kai hari a Ruwan-Godiya a daren ranar Lahadi a karamar hukumar Faskari.
Asali: Legit.ng