An kama wata mata a Kano tana yunƙurin sace yaro ɗan shekara 5 a hanyarsa ta zuwa makaranta

An kama wata mata a Kano tana yunƙurin sace yaro ɗan shekara 5 a hanyarsa ta zuwa makaranta

  • An yi ram da wata mata mai matsakaicin shekaru bayan ta yi yunkurin garkuwa da wani dalibi mai shekaru 5 a cikin Jihar Kano
  • Dalibin, Bashir Jamilu dan karamin aji ne a makarantar firamare ta Ulumuddin da ke Koki, kuma da misalin karfe 8:30 na safiyar Talata lamarin ya faru
  • Yana hanyar zuwa makarantar ne matar ta rike hannunsa tana ce masa zata sai masa nama da madara amma sai ya fara kuka

Jihar Kano - Wata mata mai matsakaicin shekaru tana hannun hukuma bayan ta yi yunkurin garkuwa da wani dalibi mai shekaru 5 a Jihar Kano, Daily Trust ta ruwaito.

Dalibin, Bashir Jamilu, dan karamin aji ne a makarantar firamare ta Ulumuddin da ke Koki a Kano.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Gobara ta yi kaca-kaca da wani gidan mai mallakar ministan Buhari

Mahaifiyar dalibin, Aisha Salisu Koki ta sanar da cewa ta tura shi makaranta da misalin karfe 8:30 na safiyar Talata amma a hanyarsa wata mata ta rike hannunsa ta ce za ta siya masa nama, indomi da madara, sai yaron ya ki yarda ya fashe da kuka.

An kama wata mata a Kano tana yunƙurin sace yaro ɗan shekara 5 a hanyarsa ta zuwa makaranta
Kano: Yadda aka damki wata mata yayin da ta ke yunkurin sace wani dalibi mai shekaru 5. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Wuraren Lungun Barebare ya fadi kasa amma ta ci gaba da jan shi. Dayake kusa da makarantar su ne, sai ya ci gaba da rokon ta akan ta sake shi amma ta ki sakin sa.

Bayan mutane sun gane ne suka yi mata dukan-tsiya

Ganin hakan yasa mutane suka fahimci abinda ke shirin faruwa suka fara tambayar ta amma sai tace dan ta ne, bayan sun fahimci ba dan ta bane sai suka rufe ta da duka.

Kara karanta wannan

Niger: Ƴan ta'addan sun kai sabon hari, sun sheƙe rai 2, sun sace sama da mutum 100

Kamar yadda mahaifiyar yaron ta shaida:

“Lokacin da na isa wurin na gan ta tana jan da na tana cewa dan ta ne, sai aka nuna mata ni aka ce ni ce asalin mahaifiyar sa.
“Bayan gani na, cikin karfin-hali ta hau duka na tana tambaya ta idan ni ce na haife shi. Duk da haka dana yana kuka yana kiran suna na inda yake cewa ‘Umma ta’.
“A nan ne na kai shi makaranta sannan wasu ‘yan sanda suka amshe ta daga hannun ‘Yan Sa Kai inda suka kai ta ofishin ‘yan sanda da ke Jakara.”

Ta kara da bayyana yadda aka wuce da matar zuwa ofishin binciken sirri daga nan aka zarce da ita bangaren yaki da garkuwa da mutane.

Mahaifiyar yaron ta yaba da kokarin ‘Yan Sa Kai

Matar ta yaba da kokarin ‘Yan Sa Kai saboda su ne suka ga matar tare da yaron sannan suka dakatar da ita.

Kara karanta wannan

Tun 2014, ba amo balle labarin ƴam matan Chibok 110, Ƙungiyar KADA

A bangaren Nasiru Ayuba Yusuf, kwamandan rundunar ‘Yan Sa Kai na Koki ya ce a lokacin da matar take jan yaron ‘Yan Sa Kan da suka gan ta sun yi zaton mahaifiyarsa ce zata kai shi makaranta tunda sanye yake da kayan makaranta.

Kamar yadda ya shaida:

“Na ce wa mutanen mu cewa su kula da kyau. Babu dadewa suka kira ni suka sanar da ni cewa mai garkuwa da mutane ce.”

A bangaren Kakakin rundunar ‘yan sanda, SP Abdullahi Haruna Kiyawa wanda ya tattauna da wakilin Daily Trust ta waya ya ce ba ya da bayanai akan lamarin amma zai kira idan ya binciko.

Wannan mummunan lamarin ya faru ne bayan makwanni kadan da Abdulmalik Tanko, shugaban wata makaranta, ya yi garkuwa da Hanifa Abubakar, dalibar makarantar sa mai shekaru 5 sannan ya halaka ta.

Katsinsa: Ɗan Shekara 22 Ya Sace Wa Dattijuwa Kuɗinta Na Garatuti Baki Daya, Ya Siya Mota Da Babur

Kara karanta wannan

Rayuwar Aure: Kotu ta datse Igiyoyin auren wata mata saboda mijin ya faɗa soyayya da kare

A wani labarin, Yan sanda a Jihar Katsina, a ranar Litinin sun yi holen wani Aliyu Abdullahi mai shekaru 22, mazaunin Kasuwar Mata Street a Karamar Hukumar Funtua saboda damfarar wata tsohuwa.

Ya wawushe mata dukkan kudinta na garatuti ta hanyar amfani da katin ta na banki wato ATM inda ya siya mota da babur da kudin, Vanguard ta ruwaito.

An taba kama mayaudarin, wanda ya kware wurin damfarar mutane ta hanyar sauya musu katinsu na ATM a baya amma daga bisani ya fito daga gidan yari kuma ya cigaba da laifin, rahoton Vanguard.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164