Borno: Zulum zai wajbata rubuta NECO a dukkan makarantun jiharsa
- Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi alkawarin yin iyakar kokarin sa wurin tabbatar da NECO ta zama wajibi ga daliban Jiharsa
- Ya mika wannan bukatar tasa ga shugaban hukumar jarabawar NECO din, Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi inda yace zai ba hukumar jarabawar hadin kan da ya dace
- Farfesa Zulum ya samu wakilcin shugaban ma’aikatansa, Alhaji Usman Jidda Shuwa wanda ya mika bukatar a ziyarar musamman da ta kai wa Farfesa Wushishi ranar Talata
Jihar Borno - Farfesa Babagana Umara Zulum, Gwamnan Jihar Borno ya yi alkawarin yin iyakar iyawarsa wurin mayar da jarabawar NECO dole ga makarantun jiharsa, Daily Trust ta ruwaito.
Ya ce yana sa ran hakan zai tabbata bisa yakinin shugaban hukumar jarabawar NECO, Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi zai amince da wajabta jarabawar ga duk makarantun gwamnatin jihar.
Farfesa Zulum ya samu wakilcin shugaban ma’aikatansa, Alhaji Usman Jidda Shuwa, wanda ya gabatar da wannan bukatar yayin da ya kai ziyara ga Farfesa Wushishi a Maiduguri a ranar Talata.
Muhimmancin jarabawar yasa ya mika wannan bukatar
A cewarsa ganin muhimmancin da NECO ta ke yi wurin bunkasa harkar ilimi a kasar nan yasa gwamnatin Jihar zata ci gaba da ba hukumar jarabawar hadin kai da tallafin da ya dace.
Yayin da ya bukaci jarabawar NECO ta tabbata a makarantu kasancewar tsawon shekaru amintacciyar jarabawa ce, za a zage wurin wayar da kan makarantun gwamnati akai da kuma tilasta dalibai yin jarabawar.
Dama tun farko shugaban hukumar ya tabbatar wa da gwamnatin Jihar cewa hukumar jarabawar a shirye take da ta bayar da hadin kai wurin bunkasa ilimi a jihar.
Ya yaba wa gwamnan akan biya wa daliban jiharsa kudin jarabawa akan lokaci tun hawan sa mulki
Yayin yaba wa gwamnatin jihar akan biya wa dalibai kudin jarabawar a kan lokaci tun hawan Zulum mulki a shekarar 2019, Daily Trust ta ruwaito yadda ya bukaci Gwamnatin Jihar Borno ta tilasta jarabawar a makarantun jihar.
A cewarsa:
“Zai burge ka idan ka gano cewa gwamnatin Jihar Borno bata cikasa yawan bukata na daliban da ake bukata a kwalejojin ilimi na kasa, don haka ake bukatar daliban makarantun gwamnatin su dinga rubuta jarabawar ta NECO.”
Babagana Zulum: Ba ni da niyyar fito wa takara a zaɓen 2023
A wani labarin, Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno ya ce baya sa ran neman wata mukamin siyasa a shekarar 2023, Daily Trust ta ruwaito.
Akwai rade-radin cewa gwamnan yana neman yin takarar kujerar mataimakin shugaban kasa a Najeriya.
Amma, da ya ke magana wurin taron tattaunawa karo na 19 da Daily Trust ta shirya a ranar Alhamis a Abuja, ya ce bai taba fatan zai zama gwamna ba ma.
Ya ce:
"Muna kara matsowa shekarar 2023 inda za a yi babban zabe, amma a wuri na bai da wani muhimmanci. Ba na fatan neman wata kujera. Ban taba fatan zan zama gwamnan Jihar Borno ba ma kuma bana fatan sake neman wata kujerar da ta fi ta amma a matsayin na na musulmi, ina addu'ar abin da ya fi alheri."
Asali: Legit.ng