Obasanjo: Sai an binciko kuma an hukunta wadanda suka banka wa gona ta wuta
- Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya yi alawadai da wadanda suka babbaka gonarsa mai hectares 2,420 ta Jihar Binuwai
- Tsohon shugaban kasa kuma soja ya kwatanta lamarin a matsayin abin takaici kuma a cewarsa, sai jami’an tsaro sun gano duk masu hannu a aika-aikar
- Dama a ranar Asabar aka samu bayanai dangane da yadda wasu batagari suka je har gonarsa ta Orchard da ke Abeokuta suka banka mata wuta
Binuwai - Tsohon shugaban kasa Obasanjo ya yi alawadai akan kona gonarsa da wasu batagari suka yi a garin Howe da ke Karamar Hukumar Gwer ta Kudu a Jihar Binuwai a kwanakin karshen makon nan, The Punch ta ruwaito.
Tsohon shugaban kasar mai shekaru 84 ya kwatanta lamarin a matsayin mummunan abu kuma ya ce sai jami’an tsaro sun gano wadanda suka tafka ta’asar.
The Punch ta ruwaito yadda batagari suka babbake gonar Orchard wacce mallakin babban mutumin ne na Hilltop da ke Abeokuta a ranar Asabar.
Dama ‘ya’yan itace yake nomawa a gonar
Tsohon shugaban kasar ya mallaki hectares 2,420 na gona a garin inda yake shuka ‘ya’yan itace kamar mangwaro da lemu.
Wasu mazauna yankin wadanda suka ce ba a biya su kudin gonar ba sun kone gonar kuma sun yi fashi tare da zane ‘yan kwana-kwanan da suka je wurin don kashe wutar.
Ya yi godiya ga wadanda suka sanar dashi batun kona gonar
Yayin tsokaci dangane da lamarin, hadiminsa na musamman a harkar labarai, Kehinde Akinyemi a ranar Talata ya ce Obasanjo ya ce gwamnatin karamar hukumar da ta jihar tare da hadin kan jami’an tsaro sun fara binciken gano masu hannu a lamarin.
A takardar mai taken ‘Obasanjo ya yi alawadai akan babbaka gonar Binuwai’, tsohon shugaban kasar ya yi godiya ga wadanda suka kira shi don masa jaje kan afkuwar lamarin.
Buhari: Na Ji Daɗin Yadda Masu Hannu Da Shuni Suka Gane Cewa Canja Najeriya Ba Aikin Mutum Ɗaya Bane
A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya yi farin cikin sanin cewa kusoshin Najeriya sun gane cewa canja kasar nan aikin kowa ne, The Cable ta ruwaito.
Kamar yadda kakakin shugaban kasa, Femi Adesina ya bayyana a wata takarda, Buhari ya yi wannan furucin ne a ranar Lahadi a wata liyafa ta girmama shugabannin kwamitin kasuwanci, siyasa, kafafen watsa labarai da sauran ma’aikata.
Dama a watan Janairun 2021 The Cable ta bayyana yadda Buhari ya zargi masu fada a jin kasar nan da kawo cikas ga gwamnatin sa.
Asali: Legit.ng