Jihar Neja: 'Yan bindiga sun sake kai mummunan hari, sun kashe sojoji 3 da mazauna da yawa
- 'Yan bindiga sun farmaki wasu garuruwa a kananan hukumomin Paikoro da Mariga na jihar Neja
- Harin wanda aka kai a tsakanin ranakun Lahadi da Litinin ya yi sanadiyar mutuwar mutane 11 ciki harda sojoji uku
- Har ila yau mutane da dama sun jikkata a harin inda aka kwashe su zuwa asibiti
Niger - Tsagerun 'yan bindiga sun kashe mutane 11 a garuruwan Neja tsakanin ranakun Lahadi da Litinin, jaridar The Nation ta rahoto.
An tattaro cewa an kashe sojoji uku da 'yan banga hudu da mazauna yankin hudu a hare-haren da suka gudana a kananan hukumomin Mariga da Paikoro na jihar Neja.
A Mariga, yan ta’addan sun kai wa sojoji da yan banga harin bazata a garin Kwanan Dutse.
An ce Jami’an tsaron na fatrol ne lokacin da yan ta’addan suka far masu. Wasu da dama sun jikkata a harin.
A karamar hukumar Paikoro, mutum hudu, ciki harda dan shekara 20 aka kashe sannan wasu da dama sun jikkata lokacin da yan ta’addan suka farmaki garuruwan Ishau, Kuna, Amale, Adunu da Kudami.
An tattaro cewa mazauna yankin sun kadu sosai domin shine karo na farko da ake kai hari garuruwan.
The Nation ta kuma ruwaito cewa da yan ta’addan, wadanda suka kai kimanin su 80 da muggan makamai sun kashe mutane fiye da haka idan ba don yan bangar da suka dakile su Sannan suka kora su zuwa cikin daji.
Wadanda suka jikkata na samun kulawar likitoci a Kafinkoro.
Ba a samu jin ta bakin kakakin yan sandan Neja, DSP Abiodun Wasiu da Shugaban karamar hukumar Paikoro, Mallam Yohana Yakubu ba, don basa daukar wayoyinsu.
‘Yan bindiga sun aika mutane 1, 192 barzahu, sun dauke 3, 348 cikin shekara 1 a Kaduna
A gefe guda, mun ji cewa a kalla mutane 1, 192 suka mutu a hannun ‘yan bindiga, sannan kuma an yi garkuwa da wasu mutum 3, 348 a jihar Kaduna a shekarar da ta wuce.
Jaridar Daily Trust ta ce gwamnatin jihar Kaduna ta fitar da wadannan alkaluma a makon nan.
Wannan bayani yana cikin rahoton harkar tsaro da aka fitar daga watan Junairu zuwa Disamban 2021 wanda kwamishinan tsaron cikin gida ya gabatar dazu.
Asali: Legit.ng