Zamfara: Sojoji da 'yan sanda sun ceto mutum 32 da 'yan ta'adda suka yi garkuwa da su
- Rundunar hadin guiwa ta sojoji da 'yan sanda a jihar Zamfara sun ceto mutum 32 da 'yan ta'adda suka yi garkuwa da su a jihar
- An gano cewa, mutane 32 da aka ceto daga hannun miyagun 'yan asalin jihohin Niger, Kebbi, Katsina da Zamfara ne
- Da yawa daga cikin wadanda aka sacen matafiya ne wadanda miyagun suka tare, tuni an mika su hannun iyalansu
Zamfara - Rundunar hadin guiwan sojoji da 'yan sanda ta ceto mutane 32 da aka yi garkuwa da su daga bangarori daban-daban na jihar Zamfara.
Yayin zantawa da manema labarai a hedkwatar su da ke Gusau, Muhammad Shehu, mai magana da yawun yan sandan jihar Zamfara, ya ce wadanda aka ceto 'yan jihohin Neja, Katsina da Zamfara ne.
Shehu ya ce:
"An kula da wadanda aka ceton yadda ya dace inda 'yan sanda suka musu tambayoyi sannan aka mika su ga iyalan su."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Premium Times ta ruwaito cewa, an ceto wadanda aka yi garkuwan da su ne a hanyar Sheme zuwa Funtua a ranar Alhamis.
"A ranar 26 ga watan Janairu, 2022 'yan sanda da aka tura hanyar Mada yayin da suke sintiri a wani gini, sun yi amfani da bayanan sirri sun ceto mutane 10 da aka yi garkuwa da su a titin da ke tsakanin Sheme zuwa Funtua a jihar Katsina, a 10 ga watan Janairu, 2022."
Wadanda al'amarin ya auku da su sun taso ne daga karamar hukumar Birnin Magaji da ke jihar Zamfara inda aka yi awon gaba da su yayin dawowa a hanya daga Legas zuwa Birnin Magaji, Premium Times ta ruwaito.
"An yi nasarar ceto wadanda aka yi garkuwan da su ne a ranar 30 ga watan Janairu, 2022 wanda yayi sanadin kubutar wasu mutane uku da aka yi garkuwa da su a kan titin Sheme zuwa Funtua a 10 ga Janairu, 2022. Biyu daga cikin wadanda aka ceton sun taso ne daga Kaduna, inda dayan ya taso daga jihar Kebbi.
"A ranar 30 ga watan Janairu, 2022 Birgediya kwamanda na Sojojin Najeriya da ke jihar Zamfara ya mika mutane 19 wadanda suka kunshi; maza 15 da mata 4 ga rundunar yan sandan jihar Zamfara.
"Jami'an sojoji ne suka ceto wadanda aka yi garkuwan da su a wuraren Dansadau da ke karamar hukumar Maru. Yayin tambayoyi ga wadanda al'amarin ya auku da su, an gano yadda yan bindiga suka sace su lokacin da suke aiki a gonakin su, bayan sun tasa keyarsu zuwa dajin Dansadau inda suka kwashe watanni biyu a hannun su," a cewarsa.
Katsinawa sun fada tashin hankali bayan an janye sojoji daga yankunan jihar
A wani labari na daban, mazauna garin Runka da wasu yankuna na karamar hukumar Safana ta jihar Katsina sun bayyana tsoron su kan makomar su bayan kwashe sojojin yankin da aka yi a ranar Litinin.
Sojoji da ke aikin hadin guiwa na tsaro suna da sansani a Runka, gari na biyu mafi girma a karamar hukumar Safana ta jihar, har zuwa jiya Litinin da aka janye su, Premium Times ta ruwaito.
Mazauna yankin sun ce 'yan ta'adda sun sanya wa Runka ido ganin irin tsaro da suke fuskanta, hakan ne kuwa ya kange su daga farmakin miyagun.
Asali: Legit.ng