Yan sanda sun ceto tsohon kansilan da yan bindiga suka sace a Nasarawa

Yan sanda sun ceto tsohon kansilan da yan bindiga suka sace a Nasarawa

  • Jami'an yan sandan jihar Nasarawa sun fafata da wasu tsagerun yan bindiga a maboyarsu
  • A yayin fafatawar, sun yi nasarar ceto wani tsohon kansila na karamar hukumar Calabar South da ke jihar Cross River, Mista Anthony Duke Effiom
  • Hakazalika sun kwato bindigar AK 47 daga hannun maharan bayan sun tsere da raunuka daban daban

Nasarawa - Rundunar yan sanda a jihar Nasarawa ta ce ta ceto wani mutum da aka yi garkuwa da shi, Mista Anthony Duke Effiom, a ranar Lahadi, 30 ga watan Janairu.

Mista Effiom ya kasance tsohon kansila a karamar hukumar Calabar South da ke jihar Cross River.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, ASP Ramhan Nansel, ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya saki a Lafia, babbar birnin jihar Nasarawa, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun yi awon gaba da ɗan uwan tsohon shugaban ƙasa a Najeriya

Yan sanda sun ceto tsohon kansilan da yan bindiga suka sace a Nasarawa
Yan sanda sun ceto tsohon kansilan da yan bindiga suka sace a Nasarawa Hoto: Premium Times
Asali: UGC

A rahoton Vanguard, Nansel ya kuma ce yan sandan sun kwato bindigar AK 47 guda daya da mujalla mara komai a ciki a jihar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce rundunar yan sandan ta samu wani kira da misalin karfe 9:30 na dare cewa wasu yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kewaye hanya a Kurmin Shinkafa wajen babbar titin Akwanga-Keffi sannan suka yi garkuwa da Mista Effiom.

A cewarsa:

“Da samun bayanin, sai kwamishinan yan sanda, Mista Adesina Soyemi ya aika takarda ga Jami’an rundunar da ke Garaku, inda ya umurci dukka tawagar dabaru na rundunar tare da hadin gwiwar Jami’an sufeto janar na yan sanda, tawagar IRT da su bi sahun masu garkuwa da mutanen.
“Don haka, a ranar 29 ga watan Janairu 2023, da misalin karfe 0100, sai Jami’an suka bibiyi masu garkuwan har maboyarsu a kauyen Angwan Maigini, inda Jami’an suka fafata da su a wani musayar wuta, daga nan sai maharan suka tsere zuwa daji a wurare daban daban da raunuka sannan yan sanda suka ceto wanda lamarin ya ritsa da shi ba tare da ya illata ba."

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun kama mutane 28, sun kwato makamai da layoyi a jihar Neja

Kwamishinan yan sandan wanda ya yaba ma Jami’an a kan kokarin da suka yi, ya gargadi miyagu da su gaggauta barin jihar ko su dandana kudarsu.

Matashi ya shiga hannu yayin da yake kokarin tserewa bayan fille kan budurwarsa

A wani labarin, rundunar yan sandan jihar Ogun ta kama wani matashi mai suna, Soliu Majekodunmi da ya tsere bayan ya jagoranci kashe budurwarsa.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, a wani karin haske da yayi kan kisan yarinyar mai suna Rofia da wasu matasa hudu suka yi a Abeokuta, ya ce an kama jagoran kungiyar, jaridar Punch ta rahoto.

Oyeyemi ya tabbatar da cewar matasan su hudu sun yanka da kuma kona kokon kan Rofia bayan saurayinta, Soliu ya yaudareta zuwa gidansa a Oke-Aregna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng