Rashin tsaro: Ni da Masari ba mu bacci idanu 2 rufe, Sarkin Katsina ga Osinbajo

Rashin tsaro: Ni da Masari ba mu bacci idanu 2 rufe, Sarkin Katsina ga Osinbajo

  • Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumin Kabir Usman, ya sanar da Farfesa Osinbajo cewa shi da Masari ba su bacci idanun su biyu rufe
  • Sarkin ya sanar da yadda farmakin 'yan ta'adda a jihar ya zama ruwan dare, ya bayyana hakan da zama babbar damuwar su
  • Osinbajo ya jaddada cewa shugaban kasa ya na kan lamarin kuma babu shakka nan babu dadewa za a ga sauyi a fannin tsaron

Katsina - Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumin Kabir Usman, ya sanar da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo cewa shi da gwamna Aminu Bello Masari ba su bacci idanunsu biyu a rufe saboda kalubalen rashin tsaro da jihar ke ciki.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Sarkin ya sanar da hakan ne yayin da Osinbajo ya kai ziyarar ta'aziyyar Hajiya Murja Mangal, mahaifiyar hamshakin dan kasuwa Alhaji Dahiru Mangal.

Kara karanta wannan

Ka nemi kujerar Buhari, mun duba maka – Mataimakin Gwamnan PDP ga Osinbajo

Rashin tsaro: Ni da Masari ba mu bacci idanu 2 rufe, Sarkin Katsina ga Osinbajo
Rashin tsaro: Ni da Masari ba mu bacci idanu 2 rufe, Sarkin Katsina ga Osinbajo. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC
"Zuwan ka yau na farko baya ga wanda ka yi yayin da ku ke kamfen gaskiya babban tarihi ne gare mu. Ka zo gida kuma ka yi mana magana kan kalubalen tsaro wanda babban damuwa ne yanzu,"
"Na dawo kenan daga Kaduna amma cike da mamaki na samu sama da wayoyi 100 kan shirin kai farmakin 'yan ta'adda, wanda hakan ya zama ruwan dare.
"Ni da gwamna ba mu da damar bacci da idanun mu biyu a rufe amma mun yi matukar farin ciki da aka ayyana miyagun nan a matsayin 'yan ta'adda," yace.

Tun farkon jawabin sa, mataimakin shugaban kasa ya ce ya yi farin cikin jin cewa halin tsaro na yankin ya na samun cigaba inda yace gwamnan ya sanar da shi hakan.

Kara karanta wannan

Jigon Arewa: Laifin 'yan Arewa ne suka sa Jonathan ya gaza karar da Boko Haram

"Shugaban kasa ya yanke shawarar ganawa da manyan kwararru a fannin tsaro kuma a tabbatar an sauya tsarin tsaron kasar inda akwai bukata.
"Ina da tabbacin cewa Mai Martaba zai tuna cewa babu dadewa shugaban kasa ya ce 'yan bindiga sun zama 'yan ta'adda. Hakan ne kawai zai bai wa hukumomin tsaro damar daukar mataki mai tsauri a kansu.
"Saboda haka ne muke fatan ganin canji kuma da izinin Ubangiji zaman lafiya zai gaggauta dawowa dukkan kauyuka da biranen Katsina da fadin kasar nan," yace.

Mataimakin shugaban kasan ya kara da cewa, da dukkan matakai da umarnin da gwamnatin tarayya ta saka a gaba, nan babu dadewa za a ga sauyi a kasar nan, Daily Trust ta ruwaito.

Tun farko Osinbajo ya kai ziyara gidan Alhaji Dahiru Mangal inda ya yi masa ta'aziyya kafin daga bisani ya karasa fadar Sarkin Katsina.

Katsinawa sun fada tashin hankali bayan an janye sojoji daga yankunan jihar

Kara karanta wannan

Na sanar da Atiku cewa ya tsufa kuma gajiye ya ke, ba zai iya shugabanci ba, Gwamnan Bauchi

A wani labari na daban, mazauna garin Runka da wasu yankuna na karamar hukumar Safana ta jihar Katsina sun bayyana tsoron su kan makomar su bayan kwashe sojojin yankin da aka yi a ranar Litinin.

Sojoji da ke aikin hadin guiwa na tsaro suna da sansani a Runka, gari na biyu mafi girma a karamar hukumar Safana ta jihar, har zuwa jiya Litinin da aka janye su, Premium Times ta ruwaito.

Mazauna yankin sun ce 'yan ta'adda sun sanya wa Runka ido ganin irin tsaro da suke fuskanta, hakan ne kuwa ya kange su daga farmakin miyagun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng