Yanzu-yanzu: EFCC ta damke babban jigon APC kan almundahanar N1.3bn

Yanzu-yanzu: EFCC ta damke babban jigon APC kan almundahanar N1.3bn

Abuja - Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta damke Dirakta Janar na Muryar Najeriya (VON) Osita Okechukwu.

Rahoto ya nuna cewa Okechukwu ya dira ofishin hedkwatan hukumar EFCC ne misalin karfe 1:30 na ranar Asabar sakamakon gayyatar da hukumar tayi masa.

Kakain hukumar EFCC, Wilson Uwujaren, ya tabbatar da maganar gayyatar Okechukwu.

Majiya ta bayyana cewa an gayyacesa amsa tambayoyi ne bisa zargin almundahanan kudi N1.3billion.

Kawo yanzu yana hannun EFCC.

Yanzu-yanzu: EFCC ta damke babban jigon APC kan almundahanar N1.3bn
Yanzu-yanzu: EFCC ta damke babban jigon APC kan almundahanar N1.3bn
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Asali: Legit.ng

Online view pixel