Harajin N24m da yan bindiga suka mana: Muna tsoron abin da zai biyo baya idan ba mu biya ba, Mutanen Zamfara

Harajin N24m da yan bindiga suka mana: Muna tsoron abin da zai biyo baya idan ba mu biya ba, Mutanen Zamfara

  • Mazauna Jihar Zamfara sun koka bayan wasikar ‘yan bindiga ta isa gare su, don yanzu haka sune suke shugabantar garuruwan da ke Jihar Zamfara
  • A cikin wasikar tasu, sun bukaci garuruwan guda 9 su biya haraji N24m idan ba haka ba zasu ci gaba da damun su da farmaki wanda dama sun saba
  • Sakamakon yadda gwamnatin Jihar bata riga ta dauki wani mataki ba, mazauna garuruwan da suka bayyana a wasikar sun fara tattara kudaden harajin

Zamfara - Mazauna kauyaku tara da ke karkashin Jihar Zamfara sun koka akan yadda ‘yan bindiga suka tura musu wasika suna bukatar makudan kudade a matsayin haraji a hannun su, Vanguard ta ruwaito.

Yanzu haka garuruwa tara ne wasikar ‘yan bindigan ta ambata wadanda tace matsawar basu tara kudaden harajin ba zasu kai musu farmaki.

Kara karanta wannan

Zamfara: An gurfanar da dillalin motocci kan zargin cin 'sassan jikin yaro' ɗan shekara 9

Yanzu haka akwai wadanda suke zaman makoki sakamakon halaka musu ‘yan uwa da abokan arzikin su da aka yi ba tare da sun aikata wani laifi ba.

Harajin N24m da yan bindiga suka mana: Muna tsoron abin da zai biyo baya idan ba mu biya ba, Mutanen Zamfara
Al'ummar Zamfara sun koka, sun ce suna fargabar abin da yan bindiga za su musu idan ba su biya harajin N24m da suka kakaba musu ba. Hoto: Channels TV
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A mawuyacin halin nan da kauyakun suke ciki, ‘yan bindigan basu dakata ba don har yanzu basu daina kisa da garkuwa da mutane ba.

Shugabannin ‘yan bindigar suke jagorantar satar jama’a musamman mata da yara suna wucewa da su dazuka, ba anan suka tsaya ba, sun fara kallafa musu haraji.

A wasikar akwai adadin kudin da suka bukaci ko wanne kauye ya biya

Kamar yadda shugabannin ‘yan bindigan suka nuna a wasikar da suka tura, sun bukaci lallai mutanen kauyakun su biya su makudan kudade ko kuma su lalata musu garuruwa ta hanyar halaka jama’a da garkuwa da wasu.

Mazaunan sun tabbatar da wasikar wacce ‘yan bindigan suka tura ta wasu mutane da suka yi garkuwa da su daga bisani suka sako su.

Kara karanta wannan

Jihar Kebbi: Yadda 'yan bindaga suka hallaka da dama, tare da sace wasu saboda kin biyan haraji

Noma ce babbar sana’ar da mazauna kauyakun suka rika, amma yanzu ba ta yuwuwa saboda ‘yan bindiga suna kai musu farmaki a gonakin su.

Hakan yasa yanzu haka wasu suka tafka asarori don hatsin jama’a da dama sun lalace a gonaki saboda tsoron kada su je girbi a sace su.

Basu dade da kai kazamin hari Anka da Bukkuyum ba

Bayan ‘yan bindigan da suka zarce 500 wadanda Bello Turji ya jagoranta sun halaka kusan mutane 200 a kauyakun da ke karkashin kananun hukumomin Anka da Bukkuyum a Jihar Zamfara, ‘yan bindigan sun bukaci kauyaku tara su biya su harajin N24m ko kuma su jiraci farmaki.

An samu bayanai akan yadda suka bukaci ko wanne kauye ya tattara daga N500,000 zuwa N5m.

Mazauna garuruwan Yargalma, Tungar Gebe, Wawan Iccen Ibrahim, Wawan Iccen Salihu, Galle, Nannarki, Ruwan Kura, Gangara da Gaude sun daina bacci saboda tsoron kada a kai musu farmaki.

Kara karanta wannan

Zamfara: Jama'a sun fada shagali da murna bayan sojoji sun ragargaza 'yan ta'adda a daji

Kamar yadda wani mazauni ya ce:

“Yan bindigan da ke zama a dajin Gando sun kai hari karamar hukumar Bukkuyum da Anka. Inda suka halaka mutane da dama kuma suka sace fiye da shanu 2000.
“Bayan sun saki wasu da suka sace, sun turo su da wasika suna bukatar haraji daga hannun kauyakun. Wasikar ta zo daga hannun kwamandojin ‘yan bindigan ne, Dogon Sabi da Auwali Wanzam inda suke bukatar harajin daga hannun jama’an.
“Wasikar wacce a cikin ta akwai lambar waya, sun ja kunnen jama’a akan lallai su biya kudaden da suka kallafa. Shugabannin anguwannin sun kai rahoto ga jami’an tsaro kuma har yanzu babu wani mataki da suka dauka.”

Kamar yadda wasikar ta zo:

“Kauyen Yargalma zasu biya N5,000,000; Wawan Iccen Ibrahim N4,000,000; Wawan Iccen Salihu N1,000,000; Gaude N1,000,000; Gelle N1,000,000; Tungar Gebe N5,000,000; Gangara N1,000,000 yayin da Nannarki da Ruwan Kura ko wanne zai biya N5,000,000.”

Tuni suka fara tara kudaden

Kara karanta wannan

'Yan bindiga da ke gudun ceto rai su na kai farmaki yankunan Zamfara, Dan majalisa

A ranar Asabar an sanar da Vanguard cewa garuruwan sun fara tara kudaden harajin.

Yayin da aka tuntubi shugaban kauyen Zugu, ya tabbatar da cewa ‘yan bindigan sun tura wasikar kuma sun bukaci ya tura sauran wasikun ga sauran kauyakun.

A cewarsa:

“An turo wasikun ne ta hannun wadanda suka sata daga bisani suka saki, inda suka bukaci a biya su haraji.”

Shugaban matasan karamar hukumar Bukkuyum ya ce sun fara tara kudade don haka ne kadai mafita tunda gwamnati ta kasa kulawa da rayuka da lafiyar jama’an yankin.

Zaharaddeen Labbo daga kauyen Ruwan Kura ya ce haka nan zasu yi biyayya ga ‘yan bindigan don tsaf zasu iya kai musu farmaki.

Sarkin Bukkuyum, Alhaji Muhammad Usman ya ce masarautar tana sane da halin da ake ciki kuma ta sanar da gwamnati da jami’an tsaro.

Har yanzu dai rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara bata ce komai ba dangane da wannan matsalar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164