NiMET: Akwai yuwuwar soke tashin jiragen sama masu zuwa Kano, Sokoto da Maiduguri
- Hukumar hasashen yanayi ta Najeriya, NiMET, ta yi hasashen cewa akwai yuwuwar soke tashin jiragen sama da suka nufa Kano, Sokoto da Maiduguri
- A cewar NiMET, tsananin buji da iska mai disashe ganin mai kallo daga nisan mita dubu daya a jihohi arewa maso yamma da na arewa maso gabas
- NiMet ta shawarci matukan ababen hawa da ke kan tituna da su kiyaye sannan masu cutar numfashi da su zauna a gida idan hakan zai yuwu
Hukumar hasashen yanayi ta Najeriya (NiMet) ta hasaso iska mai hade da kura a jihohin Arewa maso yamma da arewa maso gabas wanda ka iya dusasar da gani kasa da mita 1000, hakan zai iya dakatar da jiragen sama da jinkirin tashin su.
A hasashen da tayi na ranar Alhamis tace:
"Kakkauran kurar sanyi mai shafe ganin kasa da mita 1000 ana sa ran bayyanar ta a Maiduguri, Nguru, potiskum, Dutse, Gombe, Yola, Bauchi, Katsina, Kaduna, Zaria, Kano da Sakkwoto.
Daily Trust ta ruwaito cewa, hasashen ya cigaba da nuna cewa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Akwai yuwuwar dakatar da ayyukan jiragen sama, inda aka shawarci ma'aikatan jiragen sama da su dauki takardun jiragen sannan su bi dokokin, musamman a filayen jiragen da ke Arewacin kasar."
Hakazalika, NiMet ta shawarci masu amfani da titina da su zama masu tsananin kula yayin tuki a wuraren da ke da matsalar karancin gani a wannan lokacin, inda ta kara da shawartar mutane masu matsalar sarkewar numfashi su zama masu taka tsan-tsan.
NiMet ta bayyana yadda:
"Bujin ya taso daga Jamhuriyar Nijar da Yammacin Chadi har ta iso Najeriya inda a halin yanzu ta ke rage gani. Wannan al'amarin ana sa ran ya dauki tsawon awa 24 daga lokacin da aka bayyana hakan. Karancin ganin zai ta'azzara bayan matsalar rashin ganin da ake fuskanta a Arewa".
Daily Trust ta ruwaito yadda ake fuskantar iskar buji a duk lokacin hunturu, wanda yake rage gani lokaci bayan lokaci, musamman a Arewa.
Hakan ya zama babbar illa ga jiragen da za su tashi ko sauka arewa. Yayin da ya zama babbar matsala ga lafiya a fadin kasar
NIMET ta yi hasashen cewa mamakon ruwan sama zai hana jirage tashi
A wani labari na daban, rahoton Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NIMET) ya yi hasashen samun mamakon ruwan sama a wasu yankunan kasa daga ranar Talata har zuwa Alhamis, jaridar Aminya ta ruwaito.
A wani jawabi na hasashen yanayi da NIMET ta saki a ranar Litinin, 6 ga watan Satumba, ta bayyana cewa akwai yiwuwar samun ruwan sama kamar da bakin kwarya a jihohin Jigawa, Kaduna, Bauchi, Neja, Zamfara, Katsina da kuma Sokoto.
Rahoton ya kuma ruwaito cewa ana sanya ran samun ruwan sama matsakaici a jihohin Yobe, Kwara, Ogun, Osun, Ondo, Legas, Edo, Delta, Taraba, Adamawa daga ranar Talata, zuwa Alhamis.
Asali: Legit.ng