Atiku ya zama malamin rana daya, ya aika sako ga gwamnatin Buhari da 'yan Najeriya

Atiku ya zama malamin rana daya, ya aika sako ga gwamnatin Buhari da 'yan Najeriya

  • Atiku ya bukaci gwamnatin tarayya da ta yi kokarin sauya alkibla da tsarin ilimi a kasar Najeriya
  • Mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya yi wannan roko ne a ranar Litinin, 24 ga watan Janairu, a daidai lokacin da kasar ke bikin ranar ilimi ta duniya
  • A cewar Atiku, Ilimi wanda yace ya sauya rayuwarsa yana iya sauya rayuwar mutum, iyali da kuma al'umma baki daya

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi kokarin sauya alkibla da tsarin ilimi domin biyan bukatun kasar.

Atiku a ranar Litinin, 24 ga watan Janairu, ya bayyana cewa ilimi yana canza rayuwar mutum, iyali da kuma al’umma baki daya, inda ya kara da cewa hakan ya canza rayuwarsa.

Kara karanta wannan

Shugaba a 2023: Fulani sun yi watsi da 'yan takara daga Arewa, sun fadi zabinsu

Aiku ya magantu kan batun limi
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Ya Zama Malami, Ya Aika Sako Mai Karfi Ga Iyaye da FG | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Atiku, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2019 ya yi wannan kiran ne a daidai lokacin da Najeriya ta bi sahun sauran kasashe wajen bikin ranar ilimi ta duniya.

Tsohon mataimakin shugaban kasar a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook ya roki gwamnatin tarayya da ta sauya matakan da ake bi na ilimi domin dawo da yaran da basa zuwa makaranta zuwa makaranta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya rubuta:

"Ilimi yana sauya rayuwar mutum, iyali da al'umma, ya sauya tawa, a wannan #RanarIlimitaDuniya, ya kamata mu yi kokari don sauya al'amuranmu da kuma sauya iliminmu don biyan bukatun kasarmu.
"Muna bukatar mu fara da sauya matakin da ba a yarda da su na yaran da ba sa zuwa makaranta."

Atiku shekaru 4 kadai zai yi idan ya hau mulki, Shugaban kwamitin yakin zabensa

Kara karanta wannan

Kano: Sheikh Pantami ya yi magana kan kisan Hanifa Abubakar, ya faɗi masifun da irin haka ke jefa al'umma

A wani labarin, shugaban kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar, Cif Raymond Dokpesi, ya nemi yan Najeriya su zabi Atiku a 2023 saboda shekaru hudu kadai zai yi ya sauka.

Yace idan aka zabi Atiku kuma yayi shekaru hudu, yan yankin kudu maso gabas zasu samu daman gabatar da shugaban kasa a 2027.

Dokpesi ya bayyana hakan ranar Litinin a garin Umuahia, jihar Abia, rahoton Punch.

Asali: Legit.ng

Online view pixel