Ahmed Musa yayi martani mai zafi bayan sun sha da kyar a filin wasa a Kaduna
- Da kyar Ahmed Musa ya sha bayan wasu magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillar sun shiga filin wasa a fusace
- Kungiyar kwallon kafa ta Kano pillars ta saka kwallo a raga a minti na 85 na wasan amma sai alkalan wasa suka soke hakan
- Lamarin ya fusata magoya bayan Kano pillars kuma hakan yasa suka kutsa filin wasan da niyyar lakadawa alkalan wasa duka
Fitaccen dan wasan kwallon kafa Ahmed Musa ya nuna damuwarsa da rashin jin dadinsa a kan mummunan lamarin da ya faru a filin wasa na Ahmadu Bello dake Kaduna a ranakun karshen mako.
Kano Pillars sun karba bakuncin Akwa United a wani wasa da manyan kungiyoyin kwallon kafan suka yi.
Amma kuma magoya bayan Kano Pillars sun kutsa filin wasa a fusace domin lakadawa alkalan wasa duka bayan sun soke kwallon da ta shiga raga a minti na 85 na wasan.
KU KARANTA: Ku ajiye makamai, ku nemi yafiya da sasanci, Rundunar soji ga Boko Haram
KU KARANTA: Tsoho mai shekaru 56 da kifi ya hadiye kuma ya amayo shi, ya bada labari dalla-dalla
Abinda Ahmed Musa yace:
"Cike da takaici nake rubutu kan mummunan lamarin da ya faru. A kokarinmu na zama 'yan kasa nagari da kuma wakiltar kasarmu ta gado, wasu daga cikinmu suka yanke hukuncin yin wasan.
"Matukar zan jinjinawa alkalan wasan dake fadin kasar nan, ya zama dole in kara da cewa akwai abubuwa da ya dace mu yi saboda mu inganta wasan kwallon kafa."
Tsohon zakaran Leicester City din ya kara da cewa akwai 'yan wasan kwallon kafa masu yawa dake tunanin zuwa gida domin bugawa kungiyar NPFL wasa amma abubuwan da suka faru na iya saka musu sauyin ra'ayi.
Ahmed Musa ya kara da cewa:
"Duk da abinda na gani, na yadda cewa zamu iya cimma burinmu idan muka hada kanmu. Akwai 'yan wasa masu yawa da ke son dawowa gida kuma su yi wasa amma ganin wannan al'amarin zai iya sa musu sauyin ra'ayi.
"Abinda na sani shine, sauran 'yan wasa na son yin wasan kwallon kafa kuma su bada gudumawa ga cigaban wasanni a gida Najeriya. Idan har hakan za ta kasance, toh dole ne mu yi abinda ya dace."
A wani labari na daban, tsohon kwamandan tsageru, Mujahid Asari Dokubo, ya bayyana yadda tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya hada shi da Nnamdi Kanu, shugaban IPOB.
A wani bidiyo dake ta yawo a kafafen sada zumunta, Asari Dokubo ya kwatanta Kanu da barawo kuma ya sha alwashin maganinsa.
Ya zargi Kanu da samun riba da fafutukar Biafra tunda bashi da takamaiman aikin yi, Daily Trust ta ruwaito.
Asali: Legit.ng