Kungiyar Kirista Ta Najeriya Ta Buƙaci Buhari Ya Janye Tallafin Man Fetur Kafin 2023
- Kungiyar Kirista ta Najeriya, NCF, ta yi kira ga Shugaba Muhamamdu Buhari ya jajirce ya cire tallafin man fetur kafin 2023
- Kungiyar ta bayyana cewa wasu manya masu son karkatar da kudin Najeriya ne suka kirkiri tallafin shi yasa aka gaza gyara matatan Kaduna da PortHarcourt
- NCF din har ila yau ta yi kira ga kungiyoyin kwadago su goyi bayan gwamnatin tarayya kan cire tallafin su janye shirinsu na yin zanga-zanga
Ya zama dole gwamnatin tarayyar Najeriya ta jajirce ta ceto kasar daga rushewa ta hanyar cire tallafin man fetur, Kungiyar Kirista ta Najeriya, NCF, gammayar mabiya Katolika da Protestant ta ce.
NCF ta ce akwai alamu kwarara da ke nuna cewa idan an cire tallafin man fetur, da aka ce yana lashe kimanin Naira biliyan 250 duk wata, tattalin arzikin zai shiga mummunan hali, Guardian ta ruwaito.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A wani taron manema labarai a Abuja, shugaban NCF, Bishop John Matthew, tare da sauran shugabannin kungiyar, sun ce tallafin man fetur babban kallubale ne da ya kamata a tunkare shi gadan-gadan.
Wasu manya da ke son wawushe kudin Najeriya ne suka kirkiri tallafin mai, NCF
Kungiyar ta ce wasu manyan yan Najeriya ne suka kirkiri tallafin man feturi din domin su rika sace kudade daga arzikin kasa.
Kungiyar ta ce:
"Tsawon shekaru, an kasa gane dalilin da yasa aka gaza gyara matatan man Kaduna da Port Harcourt.
"Idan matatan man suna aiki, babu bukatar shigo da mai daga kasashen waje, hakan na nufin babu bukatar tallafin man fetur. Don haka, mun san inda kallubalen mu suke a bangaren man fetur."
Kungiyar ta yi kira ga kungiyar Kwadago ta kasa, NLC, Kungiyar TUC da sauran masu ruwa da tsaki masu zaman kansu da su goyi bayan gwamnatin tarayya a yunkurin ta na son cire tallafin man fetur.
Ta yi kira ga kungiyar kwadago na kasa ta janye zanga-zangar da ta ke shirin yi ta maye gurbinsa da tattaunawa da gwamnati.
2023: Manya masu son satar dukiyar talakawa ne ba su son a sake samun wani Buharin, Garba Shehu
A wani labarin daban, Fadar Shugaban Kasa ta ce manyan mutane masu aikata rashawa ne ba su son a sake samun 'wani Buhari' a Najeriya saboda wata manufarsu na gina kansu, Daily Trust ta ruwaito.
Mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari, Garba Shehu, cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce zai yi wahala a samu wani shugaba da zai iya zarce irin ayyukan da Buhari ya yi.
Ya yi bayanin kan dalilin da yasa Buhari ba zai 'bari a cigaba da yadda ake harka' a kasar ba a karkashin gwamnatinsa.
Asali: Legit.ng