Rashin tsaro: An bude makarantun Zamfara bayan kwashe wata 4 a garkame

Rashin tsaro: An bude makarantun Zamfara bayan kwashe wata 4 a garkame

  • Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da sake bude makarantun jihar bayan kwashe wata hudu da suka yi a garkame saboda rashin tsaro
  • Gwamnatin ta ce makarantun firamare da na sakandare da aka tantance tsaron yankunan su kuma aka gamsu ne za su koma karatu
  • Daraktoci daga ma'aikatar ilimi ta jihar za su zagaya makarantun domin duba komawar malaman da dalibai na ranar Litinin, 17 ga Janairu

Zamfara - A ranar Lahadi, gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da bude wasu makarantun firamare da sakandaren jihar daga ranar Litinin, 17 ga watan Janairu.

Sanarwar na kunshe a wata takarda da Shehu Ibrahim, mukaddashin daraktan duba inganci na ma'aikatar ilimi, Premium Times ta ruwaito.

Takardar ta ce makarantun kudi da na gwamnati da ma'aikatar ta duba kuma ta tabbatar da babu matsala za su iya komawa aiki.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 15 a wani hari da suka kai jihar Neja

Rashin tsaro: An bude makarantun Zamfara bayan kwashe wata 4 a garkame
Rashin tsaro: An bude makarantun Zamfara bayan kwashe wata 4 a garkame. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC
"Sai dai kuma, makarantun da aka bayyana cewa akwai matsala a tattare da yankunan su, za a cigaba da rufe su har sai tsaro ya inganta," Ibrahim ya sanar a takardar.

Makarantun za su koma aiki bayan rufe dukkan makarantun fadin jihar da aka yi a ranar 1 ga watan Satumbar shekarar da ta gabata, bayan an sace dalibai 80 da malamai uku na makarantar gwamnatin Kaya da ke karamar hukumar Maradun a jihar.

Daga bisani, dalibai biyar sun tsero bayan kwanaki kadan da sace su yayin da sauran 75 da malaman suka tsere daga baya.

Tun farko, 'yan ta'addan sun sace dalibai mata 279 na makarantar kimiyya ta 'yan mata da ke Jangebe, a karamar hukumar Talata Mafara a jihar, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Najeriya za ta yi nasara a yaki da rashin tsaro - Tinubu

An sako dukkan 'yan matan da 'yan ta'addan suka yi garkuwa da su a ranar 2 ga watan Maris bayan jerin sasancin da aka yi da gwamnatin jihar.

"Daga ma'aikatar ilimi, daraktoci za su zagaya domin ganin yawan daliban da suka koma makarantun," takardar tace.

Zamfarawa sun yi zanga-zanga saboda tsanantar kashe-kashe a yankunan su

A wani labari na daban, mazauna yankin Nahuche da ke karamar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara a ranar Lahadi sun yi zanga-zangar lumana a Gusau inda suka bukaci hukumomi da su tsananta tsaro a yankin kan kisan gillar da 'yan ta'adda ke yi musu.

Masu zanga-zangar wadanda suka garzaya gidan gmwamnatin jihar sun samu jagorancin tsohon shugaban karamar hukumar Bugudu, Musa Abdullahi Manager.

Ya ce ana kai musu farmaki a kowacce rana kuma ana sace jama'a inda ake karbar kudin fansa, hakan kuwa ba adalci ba ne, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Zamfarawa sun yi zanga-zanga saboda tsanantar kashe-kashe a yankunan su

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng