Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun sake kai hari Kaduna, sun tafka mummunar barna

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun sake kai hari Kaduna, sun tafka mummunar barna

  • Wasu 'yan bindiga sun sake kai hari wani yankin jihar Kaduna, sun harbe wani mutum sun sace matarsa
  • Hakazalika, rahotanni sun ce an sace wasu mutane a unguwar da lamarin ya faru da suka haura goma
  • Ya zuwa yanzu dai hukumomin tsaro a jihar da kasa baki daya basu ce komai game da wannan mummunan hari ba

Kaduna - Wasu ‘yan bindiga a kan babura, kowannen su dauke da mutum2, sun kai hari a yankin Gbagyi Villa a daren ranar Litinin din da ta gabata.

Yankin dai yana kan hanyar zuwa matatar mai ta Kaduna ne, inda suka kashe mutum daya tare da yin garkuwa da matarsa da wasu.

Hare-haren 'yan bindiga a Kaduna na kara kamari
Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun sake kai hari Kaduna, sun tafka mummunar barna | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Ya zuwa yanzu, 'yan jarida suna jiran martanin hukuma daga hukumomin tsaron kasar nan, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ci da ceto: Duk da yaye rufin gidansa domin ya biya kudin fansa, wasu na kokarin damfarar dattijo

Sai dai wani mazaunin unguwar, kuma ganau ya ce wadanda ke kan baburan sun hada da wasu ‘yan bindiga da dama da suka tsere daga yankin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

“Lokacin da suka shigo cikin jama’a, mutane suna gudu amma mutumin da ya yi kama da ‘yan banga ya tsaya yana kokarin yin waya da wani abu kamar wayar walkie talkie. ‘Yan bindigar sun harbe mutumin a ka. Ya fadi ya mutu,”

Ya yi zargin cewa baya ga matar marigayin da ‘yan bindigar suka sace, sun kuma yi garkuwa da wasu mazauna unguwar sama da 10 a wani samame da ya dauki sama da sa'a daya.

'Yan bindiga sun sace matar mataimakin shugaban fadar gwamnati

Jaridar Punch ta rahoto cewa wasu yan bindiga sun yi garkuwa da Dorcas Vem, matar mataimakin shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin Filato, Silas Vem.

Kara karanta wannan

Gwamnatina ba za ta yi watsi da ku ba: Shugaba Buhari ya yi jajen kisan 'yan Zamfara

Haka nan kuma, a wani harin na daban, yan bindiga sun sace Dakta Samuel Audu, daraktan ma'aikatar lafiya ta jihar Filato.

Majiyoyi daga fadar gwamnatin jihar Filato dake Jos, da kuma hedkwatar ma'aikatar lafiya sun tabbatar da faruwar lamarin ranar Talata.

A wani labarin, gwamnatin jihar Kaduna ta umurci dukkan makarantun gwamnati da su koma aikin kwanaki hudu a mako, yayin da za a bude makarantun a ranar 10 ga watan Janairu a zango na biyu na shekarar 2021/2022.

Kwamishiniyar Ilimi, Halima Lawal, ta ba da wannan umarni ne a Kaduna ranar Lahadi a cikin sanarwar dawowa karatu a zango na biyu na shekarar 2021/2022, Daily Nigerian ta rahoto.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya nakalto cewa, gwamnatin jihar Kaduna a ranar 1 ga Disamba, 2021, ta sauya tsarin aiki zuwa kwanaki hudu mako.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.