Maimakon mika wa 'yan sanda, 'yan banga sun hallaka 'yan leken asirin 'yan bindiga a Zamfara

Maimakon mika wa 'yan sanda, 'yan banga sun hallaka 'yan leken asirin 'yan bindiga a Zamfara

  • Wasu 'yan banga a jihar Zamfara sun hallaka wasu da zake zargin 'yan bindiga da masu kai wa 'yan bindiga bayanan sirri
  • Sun hallaka su ne bayan farautar da suke yi na ganin sun kama wadanda suka yi barna a yankin a makon jiya
  • Wannan lamari ya faru ne a karamar hukumar Kaura Namoda, yankin da ke fama da 'yan bindiga a jihar Zamfara

Zamfara - Rundunar ‘yan banga da aka fi sani da ‘Yan Sakai, ta kashe wasu da ake zargin ‘yan fashi ne su 7 a kauyen Gada da ke karamar hukumar Bungudu a jihar Zamfara, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Hakazalika, an kashe wasu mutane hudu da ake zargin suna kai wa 'yan bindiga bayanan sirri a karamar hukumar Kaura Namoda da ke jihar.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan bindiga sun bude wa mutane wuta a Zariya, sun kashe mutane

Yadda 'yan banga suka hallaka 'yan leken asirin 'yan bindiga
Yanzu-Yanzu: 'Yan banga sun hallaka 'yan leken asirin 'yan bindiga a Zamfara | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

‘Yan banga sun tare wadanda ake zargin ne a wata kasuwar wayoyin GSM da ke garin Kaura Namoda, kamar yadda Daily Nigerian ta tattaro.

An kama wadanda ake zargin, ba tare da bin ka’ida ba aka hallaka su, bayan kwanaki da ‘yan banga suka kwashe suna farautar 'yan leken asirin biyo bayan wani mummunan hari da suka kai wa al’ummar a makon jiya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A mummunan harin, an kashe hakimin gundumar da wasu mutane biyar tare da yin awon gaba da dimbin mazauna yankin da suka hada da mata da yara.

Tun da farko dai ‘yan banga sun kai farmaki garin Tuskudu mai tazarar kilomita 1 daga arewacin garin Gada, inda suke neman wani wanda ake zargi mai suna Ada da aka ce dan leken asirin 'yan bindiga ne.

Mazauna yankin sun ce an ga Ada a cikin ‘yan bindiga da suka mamaye al’ummar.

Kara karanta wannan

Garkuwa da mutane: Dakarun ‘Yan Sanda sun kubutar da mutum kusan 100 daga jejin Zamfara

Wani mazaunin garin mai suna Hafiz Sani ya shaida cewa:

“Ada ne bayyana inda maharan ya kamata su kai hari a lokacin harin.
“A gaskiya, ni na kasance daya daga cikin manyan wanda suke nema kai wa hari kasancewa ta shugaban matasa na al’umma.
“Ya kasance yana ziyartar wannan al’umma kamar wanda ba shi da laifi.
“Lokacin da ’yan banga suka game shi, sai ya bayyana wasu 'yan leken asiri sannan ya bukaci masu kashe shi da su bar wasu daga cikin wadanda ake zargin da aka kama saboda ba sa cikin 'yan leken asiri. Daga baya aka sake su.
“Ya shaida musu cewa lallai yana cikin maharan kuma yana basu muhimman bayanai kan daidaikun mutane.
“A cikin wadanda aka kashe har da wata mata mai suna Dabo Bokanya.
“Ta fada wa ‘yan banga cewa tana taimakon ‘yan ta’addan ne ta hanyar bokanci. An kuma kashe mijinta da ‘ya’yanta biyu”.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun sake farmakar jihar Kaduna, sun yi mummunan aika-aikata

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu, ya ce bai da masaniya kan lamarin, kuma ya yi alkawarin ba da bayani idan ya samu.

Buhari ya yanke hukunci na karshe kan batun samar da 'yan sandan jihohi

A bangare guda, a karo na biyu, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki amincewa da samar da ‘yan sandan yankuna, The Nation ta ruwaito.

Ya yarda da cewa jihohi da dama ba za su iya daukar nauyinsu ba kuma yana tsoron a yi amfani da su ta wata hanyar da bata dace ba.

‘Yan Najeriya da dama sun nuna bukatar samar da ‘yan sandan ciki har da gwamnonin jihohi don kawo karshen rashin tsaro da ya yi wa kasar nan katutu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.