'Yan sanda: Yadda muka ceto mata masu juna biyu daga hannun Turji a Zamfara

'Yan sanda: Yadda muka ceto mata masu juna biyu daga hannun Turji a Zamfara

  • 'Yan sandan jihar Zamfara sun sanar da cewa sun ceto mata masu juna biyu har 7 daga cikin mutum 97 da suka ceto a dajin jihar
  • Fitaccen dan bindiga, Bello Turji, tare da takwaransa Ado Aleru ne suka sako wasu mutane da suka dade a hannunsu
  • ElKanah ya sanar da cewa, 'yan sandan sun samu taimakon 'yan banga tare da tubabbun 'yan bindiga yayin da suka ceto mutanen

Zamfara - Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta ce ta ceto wasu mata masu juna biyu daga cikin mutum 97 da ta ceto daga hannun gagararren dan bindiga, Bello Turji.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Ayuba El-Kanah, ya sanar da hakan yayin da ya gabatar da wadanda aka ceto a gaban manema labarai a ranar Talata, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Zamfara: Yadda luguden jiragen NAF ya yi ajalin shugabannin 'yan bindiga da wasu

'Yan sanda: Yadda muka ceto mata masu juna biyu daga hannun Turji a Zamfara
'Yan sanda: Yadda muka ceto mata masu juna biyu daga hannun Turji a Zamfara. Hot daga dailytrust.com
Asali: UGC

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, ya ce rundunarsu da ke kananan hukumomin Shinkafi da Tsafe sun yi nasarar ceto mutum 97 da suka hada da masu juna biyu 7, jarirai masu watanni 2 zuwa 7 su 19 da kananan yara masu shekaru daga 2 zuwa 7 su 16.

"Bayan tsananin matsanta musu sakamakon luguden sojoji wurin sansanin shugaban 'yan bindiga Bello Turji a kananan hukumomin Shinkafi, Zurmi da Birnin Magaji.
“A ranar Litinin, jami'an 'yan sandan da ke yankin sun samu bayanan sirri kan cewa wasu da aka yi garkuwa da su suna shawagi a daji sun rasa inda za su nufa.
“Jami'an 'yan sandan tare da hadin guiwar 'yan banga da tubabbun 'yan bindiga sun gaggauta kama hanya inda suka samo mutum 68 daga dajin. An sace su sama da watanni uku kuma sun kunshi maza magidanta 33, yara maza 7, yara mata 3 da matan aure da suka hada da masu jego da masu juna biyu 25," yace.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun ceto daliban Islamiyya 21 daga hannun yan bindiga

Ya kara da cewa, an tsare wadanda aka sacen a kananan hukumomin Magarya, Maradun da Gusau a jihar Zamfara sai kuma Sabn Birni a jihar Sokoto.

"Har ila yau a ranar Litinin, 'yan sandan da aka tura yankin Tsafe sun yi aiki da rahotannin sirri inda suka shiga dajin Kunchin Kalgo da ke karamar hukumar Tsafe ta jihar inda suka ceto wasu mutum 29."
"An sace su sama da kwanaki sittin daga kauyukan Adarawa, Gana da Bayawuri a yankin Rijiya da ke karamar hukumar Gusau. Sun hada da mata 25 da yara maza hudu. gagararren dan bindiga Ado Aleru ne ya sace su.
"Dukkan wadanda aka ceto a halin yanzu suna samun taimakon masana lafiya daga gidan gwamnati da na hukumar 'yan sanda. Za a yi musu jawabi, a mika su hannun gwamnatin jihar kafin su koma wurin iyalansu."

Bayan neman sulhu, shugaban 'yan bindiga,Turji, ya sako mutum 52 da ya yi garkuwa da su

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Sojoji sun tarwatsa shugabannin 'yan bindiga a Zamfara

A wani labari na daban, Bello Turji, gagararren dan bindigan jihar Zamfara, a ranar Litinin ya sako mutane 52 wadanda suka dade a hannunsa, wata majiya ta tabbatar wa da Daily Trust hakan.

"Wadanda aka sako din a halin yanzu ana fito da su daga daji zuwa wani wuri da aka yi yarjejeniya inda daga nan za a kai su garin Shinkafi.
"Motoci sun yi layi kuma an umarce su da su fara tafiya hanyar Maberiya, wani yanki da ke da nisan kilomita 5 daga gabashin garin Shinkafi," wani mazaunin yankin da ya bukaci a bye sunansa ya sanar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng