Babbar Magana: Gwamnan APC zai fallasa sunayen masu ɗaukar nauyin ta'addanci a Jiharsa

Babbar Magana: Gwamnan APC zai fallasa sunayen masu ɗaukar nauyin ta'addanci a Jiharsa

  • Kwamishinan yada labarai na jihar Imo, Mista Emelumba, yace gwamna zai bayyana wa mutane sunayen masu ɗaukar nauyin ta'addanci
  • Gwamna Hope Uzodinma na jam'iyyar APC mai mulki ya jima yana ikirarin gwamnatinsa ta gano waɗan nan mutanen
  • A gobe Talata, 4 ga watan Janairu, 2022, gwamnatin Imo tace zata faɗi sunan mutanen a wurin taron masu ruwa da tsaki

Imo - Gwamnan jihar Imo, Hoe Uzodinma, zai fito fili ya bayyana sunayen masu hannu a tabarbarewar tsaro a jihar gobe Talata, 4 ga watan Janairu, 2022.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa kwamishinan yaɗa labarai na jihar Imo, Declan Emelumba, shine ya faɗi haka a wata sanarwa da ya fitar a Owerri.

A cewar Emelumba, "Gwamna zai yi amfani da taron kungiyar masu ruwa da tsaki na jihar Imo karo na shida domin faɗin sunayen masu ɗaukar nauyi da masu zuba kuɗaɗen su a matsalar tsaron jihar."

Kara karanta wannan

Akwai abubuwa masu kyau dake jiran yan Najeriya a sabuwar shekara, Gwamna Masari

Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo
Babbar Magana: Gwamnan APC zai fallasa sunayen masu ɗaukar nauyin ta'addanci a Jiharsa Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Kwamishinan yace:

"Gwamnatin jiha na da kwararan shaidu a hannun ta dake tabbatar da mutanen na da hannu kashe-kashen al'umma."

Bayan wannan me gwamnan ke shirin yi a taron?

Mista Emelumba ya kara da cewa bayan faɗin sunayen waɗan nan bara gurbin mutanen, Gwamna Uzodinma zai kuma yi jawabi kan ayyukan da gwamnatinsa ta yi cikin shekara biyu.

"Bayan fallasa sunayen waɗan nan mutanen, gwamna Uzodinma zai kuma yi wa al'ummar jihar Imo bayani kan kokarin da gwamnatinsa ta yi cikin shekaru biyu."

A wane wuri za'a gudanar da taron?

Haka nan kuma, a sanarwan kwamishinan yace an canza wurin taro daga babbar cibiyar taro ta Ahiajoku zuwa gidan gwamnatin jiha.

"A halin yanzu za'a gudanar da taron masu ruwa da tsaki a gidan gwamnatin jiha ranar Talata 4 ga watan Janairu, 2022 da misalin karfe 12:00 na rana."

Kara karanta wannan

Ko ta wane hali sai jam'iyyar PDP ta samu nasara a babban zaben 2023, Gwamna

Yace taron wanda shi ne karo na shida a jere yana da matukar muhimmanci saboda abubuwan da za'a tattauna a wurin.

A wani labarin na daban kuma Gwamna ya yi watsi da Tinubu, Atiku da Saraki, ya faɗi wanda yan Najeriya za su zaba a 2023

Gwamnan jihar Abia ya bayyana cewa lokaci ya yi da ɗan ƙabilar Igbo zai jagoranci Najeriya matukar adalci za'a yi.

Gwamna Okezie Ikpeazu, yace yana goyon bayan takarar tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Anyim, a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel