'Yan sanda sun bindige mutum 1 yayin da 'yan daba suka yi yunkurin kone fadar basarake
- 'Yan sanda a jihar Imo sun halaka dan bindiga 1 yayin da sauran suka jigata bayan yunkurin kone fadar basarake Eze Imo
- Wurin karfe 1 na rana miyagun suka zagaye fadar Dr E. C. Okeke da ke Ezioha Amaifeke a karamar hukumar Orlu ta jihar Imo
- Tuni 'yan sanda da 'yan bindiga suka sakar musu ruwan wuta, lamarin da yayi ajalin 1 daga ciki yayin da sauran suka tsere cikin daji
- An samu bindiga 1, robobin fetur 5, harsasai hudu, abu mai fashewa 1, kudi da layoyi a tare da dan bindigan da aka kashe
Imo - 'Yan sanda sun halaka mutum daya yayin da suka raunata 'yan bindiga masu tarin yawa bayan sun kai farmaki fadar Eze Imo, Dr E. C. Okeke da ke yankin Ezioha Amaifeke a karamar hukumar Orlu ta jihar Imo.
Kamar yadda kakakin rundunar 'yan sandan jihar, CSP Mike Abattam yace, 'yan bindigan sun tsinkayi fadar wurin karfe 1 na ranar Litinin, Daily Trust ta ruwaito.
"A yau, 3 ga watan Janairun sabuwar shekara wurin karfe 1 na rana, 'yan sanda tare da 'yan banga sun yi nasarar bankado wani farmaki da yunkurin kona fadar Eze Imo, Mai martaba Dr E. C. Okeke wanda wasu 'yan kungiyar IPOB/ESN suka yi yunkuri a Ezioha Amaifeke da ke karamar hukumar Orlu ta jihar Imo.
'"Yan daban masu tarin yawa sun mamaye fada basaraken dauke da miyagun makamai amma 'yan sandan sun fi karfinsu inda suka kashe daya daga cikinsu yayin da sauran suka tsere zuwa daji dauke da raunika."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Daily Trust ta ruwaito cewa, a yayin da aka duba cikin wanda aka kashe, an ga layoyi masu yawa a makale da kugunsa.
"Sauran abubuwan da aka samo daga jikinsa sun hada da kati, bam guda daya, roba biyar na fetur, kudi har dubu asirin da kuma wata bindiga mai harsasai hudu.
"A halin yanzu, 'yan sandan na duba daji domin cafko sauran da suka tsere tare da kwato miyagun makaman da ke hannunsu."
Ana ta kai farmaki tare da sace masu sarautar gargajiya a jihar, lamarin da yasa aka tura 'yan sanda domin bai wa manyan masu sarautar gargajiya tsaro a fadarsu da ke jihar.
A kalla masu sarauta biyar aka kashe a yankin inda aka yi garkuwa da wasu a cikin kwanakin nan.
Ana shirya balle gidan yarin Edo, mutum 3 sun tsere daga gidan fursunan Ilorin
A wani labari na daban, wani dan gidan gyaran hali da ke jiran hukuncin kisa da wasu ‘yan fashi guda biyu da ba a riga an yanke musu hukunci ba, sun tsere daga wani gidan yari da ke Ilorin, yankin arewa ta tsakiya a Najeriya, kamar yadda jami’an gidan yarin su ke kokarin warware zare da abawa akan balle gidajen gyaran halin da ya auku tun 2020.
Wadanda su ka tseren, Umaru Altine, wanda yake jiran hukuncin kisa saboda fashi da makamin da ya yi, sai Segun Nasiru da Isa Usman wadanda duk fashin suka yi su na jiran hukuncin kotu ne, kamar yadda jami’an suka sanar da Premium Times.
Sun tsere da safiyar Alhamis, 30 ga watan Disamban 2021 daga gidan gyaran hali da ke Mandalla a Ilorin, jihar Kwara bayan balle rodinan kurkukun kamar yadda wani jami’i ya ce.
Asali: Legit.ng