Yanzu-Yanzu: An rufe wasu makarantun Islamiyya 2 a Kaduna bayan mallami mai shekaru 50 ya ɗirka wa ɗaliba ciki
- Hukumar tabbatar da ingancin makarantu ta jihar Kaduna, KSSQA ta rufe makarantun islamiyya biyu bisa zargin cin zarafin yarinya mai shekaru 6 da kuma dirka wa wata yarinyar ciki
- Ana zargin an haike wa watar yarinya mai shekaru 6 a harabar daya daga cikin makarantun, Madrasatul Ulumul Deeniya wa Tahfizul Qur’an da ke cikin Rigasa
- Sai kuma dayar islamiyyar wacce take Tsohon Masallacin Juma’a a karamar hukumar Kachia bayan zargin wani malami mai shekaru 50 da dirka wa yarinya mai shekaru 12 ciki
Kaduna - Hukumar Kula da Ingancin Makarantun na jihar Kaduna, KSSQA, a ranar Juma'a, ta rufe makarantun Islamiyya biyu a jihar har sai masha Allahu kan zargin haikewa daliba da yi wa wata dalibar ciki, Vanguard ta ruwaito.
An rufe daya daga cikin makarantun mai suna Madrasatul Ulumul Deeniya wa Tahfizul Qur’an, a Rigasa ne kan zargin haike wa wata yarinya mai shekaru shida a harabar makarantar.
Dayan makarantar Islamiyyar kuma yana Tsohon Masallacin Juma’a ne Kachia, a karamar hukumar Kachia na jihar Kaduna, shima an rufe shi ka zargin wani mallami mai shekaru 50 da yi wa daliba mai shekaru 12 ciki.
Darektan KSSQA, Mr Idris Aliyu, wanda ya umarci a rufe Islamiyyar da ke Rigasa ya bayyana yadda aka ci zarafin ‘yar shekara shida a harabar makarantar kuma hukumar makarantar ta rufe maganar inda ta nuna kamar ba ta san hakan ya auku ba.
Bayan kakar yarinyar ta kai korafi, malamai da dalibai sun zane ta a Islamiyyar
A cewar Aliyu, ma’aikatar ta samu bayanai akan yadda kakar yarinyar ta kai korafi makarantar amma dalibai da malaman Islamiyyar suka zane ta.
Don haka a cewarsa Gwamna Nasir El-Rufai ya umarci a rufe Islamiyyar har sai an kammala bincike akan lamarin kuma an kama wanda ya yi aika-aikar kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Aliyu ya ce:
“Yanzu dai shugaban makarantar za a kama da laifin aika-aikar har sai yarinyar ta nuna wanda ya yi mata fyade kuma an yanke masa hukunci.
“Duk wanda ya daki kakar yarinyar sai ya dandana kudarsa, musamman shugaban makarantar don aikin gwamnatin jihar ne kare hakkin wanda aka zalunta.”
Shugaban makarantar, Malam Kabir Abdullahi ya musanta zargin inda ya ce ba fyade bane. Ya ce yarinyar ce ta cusa sanda a al’aurarta.
A cewar Abdullahi yanzu haka DPO din Rigasa, ASP Abubakar Bauranya ya kammala bincike akan lamarin.
DPO din ya gasgata maganar shugaban makarantar
DPO din ya tabbatar da batun shugaban makarantar Islamiyyar.
Sai dai kakar yarinyar, Hajiya Batul Gambo ta ce fyade aka yiwa jikarta kuma ta tabbatar da hakan bayan ta garzaya Asibitin Yusuf Dantsoho da ke Tudun Wadan Kaduna.
Wata takardar asibiti wacce Dr A Raji ya sa hannu ta nuna cewa tabbas fyade aka yiwa yarinyar a cewar kakarta.
Rahoton Raji ya nuna cewa al’aurarta ta ji rauni sannan kuma an kawar da budurcinta.
Yarinyar mai shekaru 12 kuma tana da ciki wata 6
Batun yarinya mai shekaru 12 da aka yiwa ciki a Kachia, Aliyu ya ce yanzu haka tana da ciki wata shida.
A cewarsa an rufe Islamiyyar bisa umarnin El-Rufai inda yace ba za a yi wasa da lafiyar dalibai ba.
Ya ce kwamishinan harkokin jama’a da ci gaba, Hajiya Hafsat Baba da kwamishinan ilimi, Hajiya Halima Lawal za su yi aiki tare da ‘yan sanda wurin bincike da tabbatar da adalci ga wadanda aka zalinta.
“Za a ci gaba da garkame makarantun har sai an kammala bincike kuma an hukunta wadanda su ka yi laifin yadda shari’a ta tanadar,” a cewarsa
Katsina: 'Yan sanda sun kama wani da ke yaudarar mata ya kwana da su a otel ya kuma sace musu waya da kuɗi
A wani labarin, jami'an yan sanda a Jihar Katsina sun kama wani mutum mai shekaru 31 da ake zargin yana amfani da intanet wurin yaudarar mata yana kwanciya da su a Kano, Vanguard ta ruwaito.
An shaida wa manema labarai cewa wanda ake zargin, Usama Tijjani, mazaunin Daurayi Quaters ne a karamar hukumar Gwale a Jihar Kano.
Yan sandan suna zarginsa da:
"Kai 'yan mata otel domin ya kwanta da su sannan ya yaudara su ya sace musu kayayyakin su masu muhimmanci".
Asali: Legit.ng