Manyan Hafsoshin Sojin ruwa na hada kai da barayi wajen sace man fetur, Hukumar Navy
Hukumar Sojin Ruwan Najeriya a ranar Alhamis ta bayyana cewa za ta saka kafar wando guda da manyan hafsoshinta dake hada baki da barayin man fetur wajen satan arzikin man Najeriya.
Babban Hafsan hukumar, Vice Admiral A.Z. Gambo, ya gargadi hafsoshinsa da cewa duk wanda aka kama da wannan laifi zai dandana kudarsa.
Ya bayyana hakan ne a taron karin girma da aka yiwa wasu manyan Hafsoshin hukumar a Abuja, rahoton Daily Trust.
A cewarsa, hukumar Navy tare da sauran hukumomin tsaro zasu cigaba da kokarin kare muradun tattalin arzikin Najeriya ta hanyoyi dakile satar danyen mai da yiwa kasa zagon kasa.
Yace:
"Duk da kokarin da mukayi wajen yaki da masu laifi, akwai daidaikun jami'ai dake hada baki da barayi wajen sace-sace."
Ya yi kira ga Sojojin da aka yiwa karin girma su zamto masu nagarta saboda na baya su fahimci cewa hukumar ba zata lamunci ayyukan batanci a tashoshin ruwa ba.
Asali: Legit.ng