Malaman addinin musulunci da kiristanci a Arewa sun bayyana wanda zasu goya wa baya ya gaji Buhari a 2023
- Limaman musulmai da na addinin kirista sun haɗa kai sun bayyana Chief Moses Ayom a matsayin ɗan takararsu a zaɓen 2023
- Limaman sun bayyana matsayarsu ne yayin da suka raka Mista Ayom zuwa gidan kwamishina mai ritaya a gidansa dake Makurdi
- A cewarsu Ayom, wanda ɗan asalin jihar Benuwai ne, ya cancanci ya jagoranci kasar nan a dai-dai wannan lokacin
Makurdi, Benue - Malaman addinin musulunci da na kiristoci na yankin arewa ta tsakiya, sun amince Chief Moses Ayom, ya nemi takarar shugaban ƙasa a zaben 2023.
Daily Trust ta rahoto cewa malaman sun bayyana matsayarsu ne ranar Alhamis, lokacin da suka raka Ayom, ɗan asalin jihar Benue, ya ziyarci tsohon kwamishinan yan sanda mai ritaya, Iorbee Ihagh, a gidansa, Makurdi.
Imam Muhammad Salisu, wanda ya yi jawabi a madadin yan uwansa musulmai, yace sun zabi Ayom ne bayan dogon nazari da shawari.
Imam Salisu yace:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Daga ƙarshe mun cimma matsaya cewa Moses Ayom shine mutumin da Najeriya ke bukata a dai-dai wannan lokaci da muke bukatar chanji nagari."
"Saboda haka ina mai alfaharin bayyana cewa baki ɗayan mu limaman yankin Arewa ta tsakiya mun amince da ɗan mu, Chief Moses Ayom."
"Mun gano cewa Mista Ayom ne nagartaccen ɗan takara a babban zaɓen shugaban ƙasa dake tafe a shekarar 2023."
Bugu da ƙari, Malam Salisu ya yi kira ga manyan yan siyasar kasar nan da suka haɗa da Bola Tinubu, Atiku Abubakar, da Bukola Saraki, su mara wa takarar Ayom baya.
Ko me malaman kiristoci suka ce?
A nasu ɓangaren, Edward William, wanda ya jagoranci malaman addinin kirista daga jihohin Arewa ta tsakiya, yace suna tare da Ayom a matsayin ɗan takarar da ya dace da Najeriya.
"Muna rokon goyon baya daga yan uwan mu na yankin tsakiya, mu aje komai a gefe, mu tallafawa ɗan mu kuma daga yankin mu, ya samu damar cimma burinsa wanda ya dace da shi."
A wani labari na daban kuma Tsohuwar hadimar gwamnan APC da mambobi sama da 100,000 sun sauya sheka zuwa PDP a jihar da APC ke mulki
Manyan jiga-jigan siyasa a APC da ANN tare da mambobi sama da 100,000 sun sauya sheka zuwa PDP a rana ɗaya.
Masu sauyan shekan sun ce hakan ya zama wajibi domin jam'iyyun da suka baro ba su iya yin abin da ya dace.
Asali: Legit.ng