Da Dumi-Dumi: Shugaba Buhari ya rantsar da sabon minista a Aso Rock

Da Dumi-Dumi: Shugaba Buhari ya rantsar da sabon minista a Aso Rock

  • Shugaban ƙasa Buhari ya rantsar da sabon karamin ministan ayyuka da gidaje, Mu'azu Sambo a fadarsa dake Abuja
  • Jim kaɗan bayan rantsar da ministan, Buhari ya shiga taron koli kan tsaro tare da hafsoshin tsaro, IGP da sauransu
  • Sambo ya karbi shahadar fara aiki ne bayan majalisar dattawan Najeriya ta tabbatar da shi a farkon makon nan

Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya rantsar da sabon karamin ministan ayyuka da gidaje, Muazu Sambo, a fadarsa dake birnin tarayya Abuja.

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da hadimin shugaban kasa, Buhari Sallau, ya fitar a shafinsa na Facebook.

Sanarwan tace:

"Shugaba Buhari ya rantsar da karamin ministan ayyuka da gidaje Muazu Jaji Sambo a fadarsa ranar 24 ga watan Disamba 2021."

A farkon wannan makon, majalisar tarayya ta amince da naɗin Mua'zu Sanbo a matsayin sabon minista, bayan shugaba Buhari ya aike musu da sunan shi.

Kara karanta wannan

Da duminsa: NCAA ta garkame babban ofishin Glo na Abuja kan bashin N4.5bn

Aso Villa
Da Dumi-Dumi: Shugaba Buhari ya rantsar da sabon minista a Aso Rock Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sambo, ya karbi rantsuwar fara aiki ne jim kaɗan kafin fara taron tsaro, wanda yanzu haka ake cigaba da gudanarwa a fadar shugaban ƙasa Aso Villa, Abuja.

Manyan mutanen da suka halarci taron

Mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, sakataren gwamnati, Boss Mustapha da mai bada shawara kan harkokin tsaro (NSA), Babagana Monguno, sun halarci wurin taron.

Sai kuma Ministan tsaro, Salihi Magashi, ministan cikin gida, Rauf Aregbesola, shugaban jami'an tsaro, Janar Lucky Irabor, hafsan sojojin ƙasa, Janar Farouk Yahaya, hafsan sojin ruwa, Awwal Gambo, da kuma hafsan sojin sama, Isiaka Oladayo Amao.

Suran sun haɗa da, Sufetan yan sanda, Usman Alƙali Baba, daraktan DSS, Yusuf Bichi, da kuma daraktan hukumar tattara bayanan sirri, (NIA), Ahmed Rufai Abubakar.

A wani labarin na daban kuma An gurfanar da tsohon gwamna kan kin bayyana neman takarar shugaban kasa a 2023

Kara karanta wannan

Aiki ga mai kare ka: Na san matsalar Mambilla, a ba ni shekara 1 a ga canji inji Sabon Minista

Wasu mutum biyu a jihar Bauchi sun gurfanar da tsohon gwamnan Abia, Orji Kalu a gaban kotu kan ya ki fara shirin takarar shugaban ƙasa a 2023.

Masu shigar da karan sun bukaci babbar kotun Bauchi ta tilasta wa sanatan ya nemi tikitin takara karkashin kowace jam'iyya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel