Yadda Kwastam Suka Kama Ganyen Wiwi Na N10.4m Da 'Yan Bindigan Katsina Suka Siyo

Yadda Kwastam Suka Kama Ganyen Wiwi Na N10.4m Da 'Yan Bindigan Katsina Suka Siyo

  • Jami’an hukumar kwastam sun yi ram dauri 250 na tabar wiwi mai kimar Naira Miliyan 10.4 a wuraren Batsari, jihar Katsina
  • Kamar yadda shugaban FOU Zone B Kaduna, A.B. Hamisu ya shaida, har kwayoyin Tramadol masu kimar naira miliyan 29.7 jami’an su ka kwace
  • Ana zargin wadanda aka kama su na hanyar kai wa shu’uman ‘yan bindigan jihar ne, don su ci gaba da amfani da su su na rura wutar ta’addanci

Jihar Katsina - Jami’an hukumar kwastam sun samu nasarar amshe ganyen wiwi dauri 250 mai kimar Naira miliyan 10.4 da ake zargin an kama hanyar kai wa ‘yan bindigar jihar, Vanguard ta ruwaito.

Su na kan hanya jami’an Hukumar Kwastam (NSC), ma’aikatan gwamnatin tarayya (FOU) na Zone B ne su ka ci karo da su.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun fito da Malaman musuluncin da suka sace bayan an biya fiye da Naira miliyan 2

Yadda Kwastam Suka Kama Ganyen Wiwi Na N10.4m Da 'Yan Bindigan Katsina Suka Siyo
Jami'an Kwastam Sun Kama Ganyen Wiwi na N10m Mallakar 'Yan Bindigan Katsina. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ba tabar wiwi kadai su ka amshe ba har da wasu kwayoyin

A cewar shugaban hukumar ta FOU Zone B Kaduna, A.B. Hamisu, sauran kayan mayen da FOU su ka amshe sun hada da: Kwayoyin Tramadol 75,582 masu kimar fiye da naira miliyan 29.7, wadanda ya ce su na kokarin amfani da su wurin ci gaba da harkar ta’addanci dasu.

Kamar yadda ya shaida:

“Yaduwar kwayoyi 1,582 na D5 masu kimar N12,720,011.68 ba ya da amfani saboda hakan zai iya haddasa ta’addanci, hakan yasa jami’anmu su ka kwace.
“An kama ‘yan ta’addan a wuraren Batsari da ke jihar Katsina ne. Kuma ina da tabbacin tabar wiwin ta su ce don an tattara ta wuri guda kuma da kyau.
“Mu na rokon jama’an gari akan ba jami’an tsaro bayanai musamman idan sun samu labarin miyagun kwayoyi ko kuma wani abu da zai iya haddasa ta’addanci.”

Kara karanta wannan

Mutanen Kaduna sun maida martani ga kalaman gwamna El-Rufa'i na aika yan ta'adda lahira

Shugaban ya bukaci bayanai masu amfani daga wurin jama’an gari

Vanguard ta bayyana yadda ya roki jama’a da su taimaka wurin ba su bayanai masu amfani. Kuma za su tabbatar sun yi iyakar kokarinsu wurin ganin sun adana bayanan don amfaninsu, kamar yadda ya yi alkawari.

An kama gungun matasa 11 da suka yi garkuwa da 'yan uwan sarki da jami'in kwastam, kuma suka kashe dan sanda

A wani labarin, Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Taraba ta samu nasarar kama wata kungiyar matasa 11 da ake zarginsu da harkar garkuwa da mutane, The Punch ta ruwaito.

Ana zargin mambobin kungiyar da halaka wani sajan din ‘yan sanda, Ogidi Habu a Jalingo tare da garkuwa da jami’in kwastom da dan’uwan sarkin Jalingo.

Wadanda ake zargin kamar yadda The Punch ta rahoto sun hada da Luka Adam, Shuaibu Nuhu, Moses Amos, Peters Mashi, Ahmadu Mallam, Adamu Mohammed, Dahiru Dalha, Gambo Isah, Sunusi Ahmadu, Mallam Mauludu da Ibrahim Idi, wadanda duk haifaffun jihar Taraba ne.

Kara karanta wannan

Muryar jami'in EFCC ya na sanar da yadda Malami ke kange masu cin rashawa ta bayyana

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164