'Yan Bindiga Sun Sace Malaman Addinin Musulunci 2 Bayan Cika Cikinsu Da Teba Da Miya Da Matar Malamin Ta Dafa
- Wasu miyagun yan bindiga sun kai hari gidan wani malamin addinin musulunci sun sace malamin tare da abokinsa yayin da suka dawo daga lakca a Ogun
- Sun tisa keyarsu zuwa cikin gida, suka kwace wayoyin kowa a gidan sannan suka shiga kitchen suka cinye teba da miya da dukkan naman da ke miyar da matar malamin ta dafa
- Rundunar yan sandan Jihar Ogun ta bakin kakakinta, Abimbola Oyeyemi, ta ce ta san da batun sace malaman kuma ta tura jami'anta yankin don ceto su
Jihar Ogun - Wasu hatsabiban yan bindiga sun sace malaman addinin musulunci biyu a Ayetoro kan hanyar Ayetoro-Abeokura a karamar hukumar Yewa-North a jihar Ogun, Daily Trust ta ruwaito.
Masu garkuwan su biyar sun yi awon gaba da Hussein AbdulJelil da abokinsa, Iliyas Mohammad Jamiu, bayan bata garin sun cika cikinsu da abinci a gidan wadanda suka sace.
An gano cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar misalin karfe 10 na dare jim kadan bayan sun dawo daga wurin wani lakca.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yayan daya daga cikin wadanda aka sace, Hussein Ibrahim, a ranar Litinin, ya ce masu garkuwar sun dauki lokaci mai tsawo a yayin da suke gidan.
Yadda abin ya faru
Ibrahim ya magantu kan yadda yan bindigan suka kwace wayoyin dukkan wadanda suke gidan, suka tafi kicin suka cinye teba da matar mai gidan ta dafa masa kafin ya dawo, tare da cinye dukkan naman da ke cikin miyar.
Ya ce:
"Ya faru ne misalin karfe 10 na dare a lokacin da (malaman) suka sakko daga motarsa Toyota Highlander wanda dan uwa na ya siya watanni biyu da suka gabata.
"Masu garkuwan su biyar ne suka zo, sun yi kwantar bauna a cikin ciyayi sannan suka kama su yayin da suka dawo.
"Bayan cafke su, sun tisa keyarsu zuwa cikin gida, suka kwace wayoyin mu, suka tafi kicin, suka dauki teba da tukunyar miya, suka ci abincin da dukkan naman da ke miyan kafin suka tafi da su."
Ibrahim ya ce masu garkuwan sun taho da muggan makamai.
Amma, ya ce masu garkuwar sun tuntube su sun nemi a biya su Naira miliyan 15 kudin fansa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Mai magana da yawun yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da afkuwar lamarin.
Yan Sanda sun ce sun baza jami'ai a daji don ceto su
Oyeyemi ya ce yan sanda da sauran hukumomin tsaro, har ma da mafarauta sun fara bincika dazuka da ke yankin.
Ya ce:
"Eh, an sanar da mu faruwar abin. Jami'an mu suna can tare da wasu har da mafarauta suna bincika daji.
"Za mu kamo su. Mun kamo wasu a Ijebu-Ode da wasu yankunan Jihar. Za mu kama su kuma za su yaba wa ayya zakinta."
'Yan bindiga sun sace babban limami da wasu mutane 10 yayin da suke sallah a Sokoto
A wani labarin, 'yan bindiga sun sace mutane 11 ciki har da babban limami, Aminu Garba, wanda ke shirin jagorantar mutane yin sallah Juma'a a jam'i a kauyen Gatawa da ke karamar hukumar Sabon Birni a Jihar Sokoto.
An sace limamin tare da wasu mutane uku ne a ranar Juma'a kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Maharan sun tare hanyar Sabon Birnin zuwa Gatawa a ranar Asaba, inda suka bindige mutane uku suka kuma sace wasu mutanen bakwai.
Asali: Legit.ng