Rubutu a Facebook: Kotu ta bada belin hadimin Goje bayan tsare shi tsawon kwana 20

Rubutu a Facebook: Kotu ta bada belin hadimin Goje bayan tsare shi tsawon kwana 20

  • Alkalin wata kotun majistare da ke Gombe ya bayar da belin Muhammad Adamu Yayari, sabon hadimin Sanata Muhammad Danjuma Goje, na fannin yada labarai
  • Yayari ya na hannun ‘yan sanda tun ranar 30 ga watan Nuwamba bayan yin wata wallafa a shafinsa na Facebook a kan murabus din wasu masu mukami a jam’iyyar APC
  • A ranar 25 ga watan Nuwamba ne aka zarge shi da yin wata wallafa ta karya akan ‘yan jam’iyyar APC na karamar hukumar Yamaltu/Deba wacce hakan ya ja masa matsala

Jihar Gombe - Alkalin wata Kotun Majistare da ke jihar Gombe ya bayar da belin sabon hadimin Sanata Muhammad Danjuma Goje a ranar Litinin, Daily Trust ta ruwaito.

Yayari ya na hannun ‘yan sanda tun ranar 30 ga watan Nuwamba bayan yin wata wallafa a shafinsa kan murabus din wasu masu makamai a jami’iyyar APC daga karamar hukumar Yamaltu/Deba.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Kotu ta soke kasancewar dan takarar APC a zaben gwamnan Anambra

Rubutu a Facebook: Kotu ta bada belin hadimin Goje bayan tsare shi tsawon kwana 20
Bayan shafe kwana 20 a tsare, kotu ta bada belin hadimin Goje. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Lauya mai kara, Barista Ramatu Ibrahim Hassan, ta sanar da kotu yadda wanda ake zargin a ranar 25 ga watan Nuwamban 2021 ya yi wata wallafa ta bogi akan wasu masu mukami a jam’iyyar APC a karamar hukumar Yamaltu/ Deba a shafinsa na Facebook.

Lauyar ta ce wallafar ta sa ta tayar da tarzoma

Barista Hassan wacce ta karanta rahoton ‘yan sanda, inda ta ce wanda ake zargin ya yi hakan ne don cutar da ‘yan jam’iyyar bisa cewa kaso 80% din masu mukaman sun yi murabus daga kujerunsu.

Daily Trust ta rahoto yadda ta sanar da kotu cewa Yayari ya kawo rikici saboda wallafar, wanda ya ci karo da sashi na 393 da 114 na dokar Penal Code.

A bangaren wanda ake kara, barista Luka Haruna ya bukaci a bayar da belin wanda ake kara saboda rashin lafiyarsa.

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban kasa ta jero tulin nasarorin Shugaba Buhari yayin da ya cika shekara 79

Alkalin ya bayar da belin yayin da ya bukaci wanda ake kara ya gabatar da tsayayyu biyu

Yayin da alkalin kotun, Chief Magistrate Mohammed Suleiman Kumo ya gama sauraron karar, ya amince da bayar da belinsa.

A cikin sharuddan belin, alkalin ya bukaci wanda ake kara ya gabatar da tsayayyu guda biyu.

Ya ce wajibi ne daya daga cikin tsayayyun ya kasance mazaunin Gombe yayin da dayan zai zama shugaban gargajiya.

Kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 21 ga watan Fabrairun 2022, don ci gaba da shari’ar.

Abidemi ya fadi hakan ne a Abuja ranar Litinin inda ya ce bai dace ba yadda mutane su ka dinga rubutu marasa kyau akan shugaban kasar duk da kokarinsa akan Najeriya

EFCC ta bukaci kotu ta tura Fani-Kayode gidan yari kan zarginsa da gabatar da takardun asibiti na bogi

A wani labarin, Hukumar yaki da rashawa, EFCC a ranar Juma’a ta gurfanar da tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode, bisa zarginsa da amfani da takardun asibiti na bogi.

Kara karanta wannan

Yadda wani mutum ya rasa ransa wurin satar wayoyin transifoma a Gombe

Fani-Kayode ya bayyana gaban kotun laifuka na musamman da ke Ikeja bisa zarginsa da aikata laifuka 12 kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Vanguard ta ruwaito yadda Fani-Kayode ya musanta duk zargin da ake masa cikin laifukan har da yaudara, amfani da takardun bogi, kirkirar shaidar bogi tare da amfani da shaidar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164