EFCC ta bukaci kotu ta tura Fani-Kayode gidan yari kan zarginsa da gabatar da takardun asibiti na bogi

EFCC ta bukaci kotu ta tura Fani-Kayode gidan yari kan zarginsa da gabatar da takardun asibiti na bogi

  • Hukumar yaki da rashawa ta gurfanar da tsohon ministan sufurin jiragen sama sama, Femi Fani-Kayode bisa zarginsa da amfani da takardun asibiti na bogi
  • Fani-Kayode ya gurfanar gaban kotun laifuka na musamman da ke Ikeja saboda laifuka 12 inda duk ya musanta laifukan da ake zarginsa da su
  • Kotun ta bayar da belinsa bisa sharadin biyan naira miliyan biyar tare da gabatar da tsayayye wanda gidansa zai kasance kusa da kotun

Jihar Legas - Hukumar yaki da rashawa, EFCC a ranar Juma’a ta gurfanar da tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode, bisa zarginsa da amfani da takardun asibiti na bogi.

Fani-Kayode ya bayyana gaban kotun laifuka na musamman da ke Ikeja bisa zarginsa da aikata laifuka 12 kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Waiwaye a 2021: Haziƙan Ɗaliban Najeriya 4 Da Suka Karya Tarihin Da Ba a Taɓa Zaton Wani Zai Iya Ba

EFCC ta gurfanar da Fani-Kayode gaban kotu bisa zarginsa da amfani da takardun asibiti na bogi
EFCC ta gurfanar da Femi Fani Kayode a kotu kan zarginsa da gabatar da takardun asibiti na bogi don gudun shari'a. Hoto: Vanguard
Asali: Facebook

Vanguard ta ruwaito yadda Fani-Kayode ya musanta duk zargin da ake masa cikin laifukan har da yaudara, amfani da takardun bogi, kirkirar shaidar bogi tare da amfani da shaidar.

Yayin da ya musanta laifukan da ake zarginsa da su, lauyan EFCC, S. I. Suleiman, ya bukaci kotu ta samar da ranar sauraron karar.

Lauyan EFCC ya nemi kotu ta daure tsohon ministan

Ya kuma bukaci kotu ta tura tsohon ministan gidan gyaran hali.

Lauyan Fani-Kayode, Wale Balogun ya bukaci kotu ta bayar da belinsa kamar yadda sashi na 115(2) na Administration of Criminal Justice Law, 2021 kamar yadda aka gyara ya tanadar.

A cewarsa, tun shekarar 2016, ya ke shari’a gaban alkalai biyu a babbar kotun jihar Legas kuma ya cika duk wasu sharuddan beli.

Kara karanta wannan

Alkali ya fallasa lauyan da yayi yunkurin ba shi cin hanci a Plateau

Balogun ya kula da yadda Fani-Kayode ya gabatar da fasfotinsa na kasar waje ga babbar kotun tarayya a matsayin daya daga cikin sharuddan belinsa.

Kamar yadda ya shaida:

“Tun da aka fara bincike akan wannan lamarin, EFCC ta gayyace Fani-Kayode a ranar 23 ga watan Nuwamba wanda ya sha tambayoyi na sa’o’i bakwai sannan su ka bayar da belinsa.
“An sake shi sannan na rubuta takardar tabbacin zan taho kotu da shi a duk lokacin da aka bukaci hakan.
“Duk laifukan da ake zarginsa da su za a iya bayar da belinsa, kuma horonsu tsakanin shekaru uku ne zuwa bakwai a gidan yari. Mu na so alkali ta yi amfani da matsayinta ta hanyar amincewa da bukatar wanda ake kara.”

Alkali ta amince da belinsa

Lauyan ya kula da cewa Fani-Kayode ya yi minista har sau biyu ga gwamnatin tarayyar Najeriya sannan shekarunsa 61.

Yayin bayar da belinsa, Justice O.O Abike-Fadipe ta ce EFCC ba ta nuna rashin amincewarta da bukatarsa ba.

Kara karanta wannan

Sabuwar dokar tattali za ta sa rashin biyan haraji ya kai mutum kurkuku na tsawon shekara 5

Don haka alkalin ta bukaci ya biya naira miliyan biyar na beli sannan ya rubuta takardar yarjejeniya akan cewa zai bayyana gaban kotu a duk lokacin da za a sake zama akan shari’ar.

Har ila yau, zai gabatar da tsayayye wanda zai kasance mazaunin kusa da kotun ne sannan shi ma ya biya Naira miliyan biyar, a cewar alkalin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel