Yanzu kam lokaci ya yi da ya kamata kowa ya nemi makami, gwamna Masari ya magantu
- Gwamnan jihar Katsina ya jaddada cewa, ya kamata gwamnatin Najeriya ta bari 'yan Najeriya su fara rike makami
- Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da ya ziyarci jihar Sokoto tare da wasu jiga-jigan yankin Arewa maso yammaci
- Ya kuma bayyana cewa, bai kamata a bari 'yan ta'adda su ci gaba da hallaka wadanda basu ji ba basu gani ba
Sokoto - A wani mataki na dakile yaduwar matsalar rashin tsaro musamman a yankin Arewa maso yammacin kasar nan, shugaban kungiyar gwamnonin arewa maso yamma, Aminu Bello Masari, ya bukaci a ba wa ‘yan kasar damar rike makamai domin kare kansu.
Masari, wanda shi ne Gwamnan Jihar Katsina, ya ce sam ba abin yarda ba ne a bar masu laifi su rike makamai su rika kai hari da kashe mutanen da basu ji ba basu gani ba.
Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da ya jagoranci wasu takwarorinsa na yankin a ziyarar ta’aziyya ga Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal da al’ummar Jihar.
Ya jaddada cewa magance matsalar rashin tsaro ba shi da alaka da addini ko kabilanci, Tribune ta ruwaito.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce:
"Muna bukatar wata hanya da ba a saba da ita ba don tunkarar wadannan mutanen da ba komai ba ne illa dabbobi da ke addabar mutanenmu a fadin kasar nan."
Ya yi kira da a hada kai da shugabanni da ’yan kasa domin su kwata dukkan dazuzzukan da ke fadin kasar nan daga ‘yan bindiga da sauran miyagun ayyuka, inji rahoton This Day.
A nasa jawabin, gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya kuma bayyana dazuzzukan da aka kebe musamman a Arewacin kasar nan a matsayin mafakar miyagu.
Ya ce kiran da a ke yi na a kwato dazuzzukan a yanzu ya kamata a yi, “ba batun noma ko farauta ba ne a dajin mu kawai dai mu mallaki dajin gaba daya.” Ya kara da cewa.
Da yake mayar da martani, gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya yabawa gwamnonin da mukarrabansu bisa samun lokacin ziyarar jiharsa a wannan lokaci.
Ya bayyana ‘yan bindigar da ke kashe mutane a matsayin miyagu wadanda ba su da tausayi ko manufa sai dai su kai hari ba tare da la’akari da addini ko tsagin siyasa ba.
Ya kara jaddada kiransa ga shugaba Buhari da ya kafa dokar ta-baci a yankunan da ‘yan bindiga suka mamaye a kasar.
Ya ce hakan zai taimaka wa sojoji wajen magance 'yan bindigan da kuma ji dasu da yaren da suka fi fahimta.
Gwamnan Zamfara ya tafi neman taimakon shugaban Nijar kan batun 'yan bindiga
A wani labarin, Gwamna Bello Mohammed Matawalle na jihar Zamfara, a ranar Litinin, ya gana da shugaban jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum, a wani bangare na kokarin kawo karshen duk wani nau'in 'yan bindiga a Najeriya da Jamhuriyar Nijar.
Sakataren yada labarai na gwamnan, Jamilu Iliyasu Birnin Magaji, ya ce shugabannin biyu sun gana ne a fadar shugaban kasa dake Yamai, Daily Trust ta ruwaaito.
Gwamna Bello Matawalle ya samu rakiyar Sanata Sahabi Yau Kaura mai wakiltar mazabar Zamfara ta Arewa da dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Gummi/Bukkuyum a majalisar wakilai ta tarayya, Injiniya Suleiman Abubakar Mahmoud Gummi.
Asali: Legit.ng