Ya karbi bashin N400,000 hannu na ashe auren wata zai yi da su: Budurwa ta tona asirin saurayi

Ya karbi bashin N400,000 hannu na ashe auren wata zai yi da su: Budurwa ta tona asirin saurayi

  • Wata budurwa yar Najeriya ta bayyana hotunan saurayin da suka kwashe shekaru biyu suna soyayya amma ya yaudareta
  • A cewarta, ana sauran makonni biyu daurin aurensa da wata yarinyar daban ya daina daga wayarta
  • Ta kara da cewa ta bashi aron kudi dubu dari hudu ashe kayan auren wata budurwar ya je yi da su

Wata budurwa ta tada zaune tsaye a kafafen sada zumunta inda ta bayyana hotunan wani saurayinta da ya yaudareta bayan shekaru suna soyayya.

Yarinyar mai suna @fine_stefany1 a Tuwita ta daura hoton mutumin da sabuwar amaryarsa inda tace shekarun biyu suna soyayya.

Budurwa ta tonaasirin saurayi
Ya karbi bashin N400,000 hannu na ashe auren wata zai yi da su: Budurwa ta tonaasirin saurayinta Hoto: @therattleroomng
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Budurwa mai shekara 22 za ta yi wuff da tsoho mai shekara 76, tace babu gudu ba ja da baya

Ana saura makonni biyu auren ya daina daukan wayarta

Ta bayyana cewa mutumin ya daina daga wayarta kuma ya daina amsa sakonnin da take tura masa ana saura makonni biyu daurin aurensa da wata yarinyar daban.

Hakazalika hakan ya biyo bayan bashin N400k da ya karba hannunta kuma ta gano ashe ayan auren ya saya da su.

A jawabin, @thetattleroomng ta ruwaito da cewa:

"Mun kwashe kimanin shekaru biyu muna soyayya, mutumin nan yayi aure karshen makon da ya gabata, ya daina amsa kirar na da sakonni na ana saura makonni biyu auren."
"Kuma ya karbi bashin 400k hannu na don shirye-shiryen aure, ko sau daya ban ga alaman zai yi aure ba, amma babu abinda ke boyuwa har abada a rayuwa."

Daga baya ta sake daura sabon jawabi cewa ya biya ta kudin yanzu.

Yan Najeriya sun yi tsokaci

Ummusalama Momcy:

"Insha Allahu abinda yay miki sai an nika masa abinda yay miki akan "yayansa"

Kara karanta wannan

Ba Kayan Matan Jaruma Ne Ya Raba Aure Na da Laila Ba, Baƙin Halinta Ne – Biloniya, Ned Nwoko

Gen Yakubu S Abubakar:

"Kambu amma wannan PH.D ne dashi do Allah kubani number sa
Ke kuma kiyi hakuri kada kici mutuncinsa meyuwa yaya ta biyu dake."

Nura Isa S Garo:

"Kiyi hakuri ki fauwalawa Allah daman Allah yayi ke ba matarsa bace, yamayi kokari da kika sani sauran sati biyu ni tawa sauran kwana biyu abokina ya kawomin invitation din daurin aurenta nican inata shire shirye ashe ita harta wuce wajen."

Jaafaru Somai Sonka Lafiya:

Allah ya kara ke kika sake da kin nuna masa auren ne a gabanki da baku dauki digon lokaci kuna shire ba

Uth S Musa:

"Allah ya saka Miki xakiga yadda karshen auren xexama. Kawai ki saka musu idanu Allah baya xalunci Kuma baxe bar xalunci ya tabbata ba, kiyi hakuri akwai lokaci."

Asali: Legit.ng

Online view pixel